1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin rigingimu a Sudan

September 4, 2011

Mutane 17 sun mutu a Sudan sakamakon sabbin rigingimu a yankin Blue Nile da kudancin Kordofan

https://p.dw.com/p/12SpU

Mutane 17 suka hallaka lokacin wata arangamar da ta afku tsakanin dakarun Sudan da wasu 'yan tawayen da ke da alaka da Kudancin Sudan a ɗaya daga cikin jihohin da ke kan Iyakarta da sabuwara kasar ta kudanci Sudan. Hukumar kula da masu gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta rawaito ranar asabar cewa kimanin mutane dubu uku suka kauracewa yankin sakamakon rigingimu. Haka nan kuma hukumar ta yi kira da a kai tallafin gaggawa domin daƙile rikicin wanda ka iya kai ga kisan kare dangi. Masana a Sudan sun ce gwamnati a Khartoum na ƙoƙarin daƙile duk harkokin 'yan tawaye ne a jihohin da ke kudancin Kordofan da Blue Nile kafin su zama ƙungiyoyi masu karfi, su kuma sami aƙidun da ka iya zama barazana ga ɗorewar gwamnatin ta Sudan bisa la'akari da ballewar da Kudancin Sudan ta yi.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Abdullahi Tanko Bala