1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan kullen Corona a Turai

Abdullahi Tanko Bala
November 1, 2020

Yayin da cutar corona ke cigaba da yaduwa a nahiyar Turai kasashe da dama a nahiyar sun kakaba sabbin matakan kulle domin dakile yaduwar cutar wadda kawo yanzu ta halaka mutane kusan 2,000 a yankin.

https://p.dw.com/p/3kjAb
Deutschland München | Coronavirus | Oper, leeres Restaurant
Hoto: Andreas Gebert/Getty Images

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sanar da daukar tsauraran matakan kulle na makonni hudu daga ranar Alhamis mai zuwa.

A halin da ake ciki kasar Austria ta sanar da samun bullar a karon farko cikin watanni inda ta sanya dokar takaita zirga zirgar jama'a daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe.

A kasar Girka alkaluman masu kamuwa da cutar a kullum ya haura mutum 2000 karon farko tun bayan bullar cutar. Gwamnatin ta kafa dokar kulle tun daga ranar Talata inda gidajen sayar da barasa da kantunan shayi da gidajen cin abinci da kuma wuraren motsa jiki duk za su kasance a rufe a fadin kasar har zuwa karshen watan na Nuwamba.

Kasashen Portugal da Jamus da Faransa su ma sun kafa kwarya kwaryar dokar kulle domin dakile yaduwar cutar ta Corona.