1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Kwango

Sabbin hare-hare a Kwango sun salwantar da rayuka

June 20, 2024

Hare-hare a arewacin Kwango sun hallaka wasu fararen hula, hare-haren da aka dora wa 'yan tawayen kasar. KWangon dai ta fada cikin rikicin tawayen ne tun a 2012.

https://p.dw.com/p/4hJer
Wata cikin dimuwa a lokacin tashin bam a Kwango
Wata cikin dimuwa a KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Akalla mutane biyar aka tabbatar da cewa sun mutu a wannan Alhamis a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a wani harin boma-bomai da aka dora alhaki kan mayakan tawayen M23 a arewacin lardin Kivu.

Mace-mace da ake gani a Kwango dai na nuna karuwar tabarbarewar al'amurea ne a yakin da gwamnatin kasar ke yi da mayakan na tawayen da ke samun goyon bayan gwamnatin Ruwanda.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, rikicin na Kwango ya tilasta wa fararen hula sama da miliyan daya da dubu 500 rabuwa da muhallansu.

Rikicin na tawaye wanda ya faro a tsakanin shekarun 2012 zuwa 2013, ya kara ta'azzara ahalin bukatar agajin jinkai a musamman lardin na Kivu da ke arewaci, kuma babu alamun samun sauki saboda kasancewar rikice-rikice a kasashen Ruwanda da kuma Yuganda yau kusan shekaru 30.