Sabani tsakanin Amirka da China kan Chen Guangcheng
May 4, 2012Dan gwagwarmayar kare hakkin jama'a na kasar China, Chen Guangcheng, wanda kuma makaho ne, ranar Alhamis, lokacin tattaunawa ta wayar tarho da yan majalisar dokokin Amerika, ya nemi kasar ta bashi mafakar siyasa. Yace ina son zuwa Amerika, inda zan huta, hankalina yakwanta, inji, lokacin zantawa da yan majalisar na Amerika daga gadon asibiti, inda yake kwance a birnin Peking. Chen an kai shi asibitin ne bayan da a wani yanayi mai ban-mamaki, ya tsere daga ofishin jakadancin Amerika, inda yake karkashin daurin talala. Hakan ya kawo wani sabon sabani a dangantaka tsakanin Amerika da kasar ta China.
A ranar Alhamis din Chen ya sami damar magana ta mintoci da dama ta wayar tafi-da-gidanka da yan majalisar dokokin Amirka a Washington daga gadon asibitin sa a Paking, inda aka sami mai fassara tsakanin su a lokacin wayar.
Ina son saduwa da Hilary Clinton, inji dan gwagwarmayar na kasar China da yake baiyana rokon sa ga yan majalisar da suka saurare shi lokacin wata muhawara da suka yi game da kasarta China.
Chen Guangchen ya baiyana fata mai karfi ta samun goyon baya daga sakatariyar harkokin wajen ta Amirka, kuma yace yana so ido da ido ya godewa Hilary Clinton, wadda ma har ya zuwa ranar Jumma'a da safe ta kasance a birnin Peking tana shawarwari.
Chen yana son saduwa da Clinton ne saboda burin sa shine ya kasance shi da yayan sa da matarsa su kasance cikin jirgin dake dauke da sakatariyar harkokin wajen ta Amerika, yadda ba tare da wani jinkiri ba zasu fice daga China. Shi kansa Bob Fu, da ya fassara maganganun da Chen yayi da yan majalisar dokokin, babban abokine kuma makuncin dan gwagwarmayar neman hakkin jam'ar, kuma shine shugaban kungiyar kare hakkin jama'a mai suna ChinaAid mai mazaunin ta a Texas. Fu ya shaidawa majalisar dokokin ta Amirka irin abubuwan da Chen ya sanar dashi cewar sun gudana a wannan mako a ofishin jakadancin na Amirka a Peking.
Idan har baka fice daga ofishin jakadancinmu ba, inji Amirkawan a gaban Chen, to kuwa ba zaka sake samun wata dama ta ido hudu da matarka ba, ko yayanka biyu. Chen ya shaida mani cewar a sakamakon wwannan barazana, ya tsinci kansa cikin wani halina kaka-ni-kayi, inji Fu, dake jawabi a gidan television na CNN, inda ya kuma kara da cewa: Chen ya kasance a wani hali na tsaka-mai-wuya, bai kuma san abin da zai yi ba.
Kungiyar kare hakkin yan Adam ta ChinaAid da shugaban ta Fu, sun zargi ofishin jakadancin Amirka a Peking da laifin matsa lamba da kuma baiwa dan gwagwarmayar na China damar fita daga ofishin na jakadanci. Fu yace babban kuskure ne Chen bayan kwanaki shida kawai a nemi ya bar ofishin jakadancin. Da kamata yayi a bashi karin lokaci. Yanzu haka dai ana samun karuwar masu sukan manufofin Airka kan kasar ta China. Mitt Romney abokin takarar Barack Obama, ya zargi shugaban na Amirka mai ci da laifin yiwa gwamnati a Peking sasauci fiye da kima.
Idan rahotanni game da halayen da ofishin jakadancin Amerika Peking ya nuna suka tabbata gaskiya,, to amma wannan rana ta zama mai muni ga batun yanci.
A maida martani, kakakin Obama yace shugaban na Airka yana daukar matsalar ta Chen da gaske matuka, to sai dai baya son bata zumunci da dangantaka a fannoni da dama dake tsakanin Amirka da kasar ta China.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar