1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban shugaban ƙasar Somaliya ya ƙetara rijiya da baya

September 12, 2012

Al-Shebab ta kai hari a ofishin zaɓɓaɓen shugaban ƙasar Somaliya Cheik Hasan Mahmud

https://p.dw.com/p/167bo
Somali government soldiers patrol the scene of an explosion in the capital of Mogadishu September 12, 2012. Somalia's al Shabaab rebels carried out a bomb attack on Wednesday that targeted a Mogadishu hotel where the president and Kenya's visiting foreign minister were holding a news conference, the group said. REUTERS/Omar Faruk (SOMALIA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS SOCIETY)
Hoto: Reuters

Saban shugaban ƙasar Somaliya Hasan Cheik Mahmud da aka zaɓa ranar Litinin da ta wuce ya ƙetare rijiya da baya.A yau wasu 'yan ƙunar baƙin wake sun yi amen wuta a cikin Hotel dake birnin Mogadiscio, wadda kuma ke matsayin fadar shugaban ƙasa.

An kai wannan hari a yayin da shugaban ke ganawa da ministan harkokin wajen Kenya Samson Ongeri.

Tawagar sojojin ƙungiyar tarayya Afrika dake gadin shugaban, ta ce Hasan Cheik Mahmud bai jimu ko ƙwarzane ba.

Saidai duk da wannan hari,a cewar Husaini Bantu wani ɗan Majalisar Dokokin Somaliya, ƙasar ta kama hanyar komawa kan doka da oda, kuma mutanen da suka ƙaurace sun fara komawa gida:

"Ina fatan shugaban ƙasa zai ɗauki dukan matakan da suka wajaba domin baiwa 'yan gudun hijira damar komawa gidajensu, domin mu gama ƙarfi mu sake gina Somaliya."

Kungiyar Al-Shebab ta ɗauki alhakin kai wannan hari, kuma ta yi alƙawarin ci gaba da gwagwarmaya har ta sai ta ƙwace ƙasar Somaliya gaba ɗaya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe