1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban jadawallin zabe a Masar

October 2, 2011

Bisa matsin lambar masu zanga-zangar neman sauyi,komitin Koli na sojojin da ke gudanar da mulki a Masar ya bayyana wani saban jadawallin zabe

https://p.dw.com/p/12kaP
Hoto: picture-alliance/dpa

Komitin koli na sojojin dake jagorantar rikwan kwarya a kasar Masar sun bayyana sabuwar taswirar shimfida tsarin mulkin demokradiya a kasar.Shawarar da sojojin su ka bada, ta tanadi shirya saban zaben raba gardama na saban kundin tsarin mulki a watan Maris zuwa Afrilu na shekara mai kamawa.Sannan zaben shugaban kasa zai biwo baya watani 18 bayan zaben saban kudin tsarin mulkin.

Da farko dai sojojin na Masar, sun yi alkawarin sauka daga mulki a tsukin watani shidda bayan kifar da shugaba Hosni Mubarack.

A nasu gefe dubunan misirawa ke cigaba da zanga-zanga a dandalinTahrir, domin nuna takaici game da tafiyar hawainiya da sojojin ke yi wajen tabbatar da cenji a kasar Masar.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman