Sa in sa tsakanin Siriya da Turkiya
June 25, 2012Talla
Ƙasar Siriya ta gargaɗi ƙungiyar tsaro ta NATO da kadda ta kuskura ta kai ga ɗaukar matakin na fansa;sakamakon kakabo jigirgin sama na ƙasar Turkiya da mayaƙan Siriya suka yi, wanda suka ce ya keta sararin samiyar su.Siriya dai ta yi wannan furci ne gabannin taron ƙungyar tsaron ta NATO da zai gudana a gobe talata domin tattauna batun,
To a share ɗaya kuma rahotannin daga Siriyan na cewar wani babban hafsan soji da wsasu sojoji guda 33 na gwamnatin Siriya sun yi marabus sun kuma shiga cikin ƙasar Turkiya:
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala