1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalar rushewar gine-gine

November 2, 2021

Rahotanni daga jihar Legas a Najeriya, na nunar da cewa hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane a ruftawar bene mai hawa 25 a Ikoyi.

https://p.dw.com/p/42U3A
Nigeria eingestürztes Hochhaus  in Lagos
Jami'an agaji na kokarin tsakulo wadanda suka rage da rai, bayan gini ya rufta a LagosHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Sai dai 'yan uwan wadandan abin ya shafa na korafin tafiyar hawainiya na aikin ceto sauran mutanen, koda yake wasu na yabawa da irin kokarin da a ganinsu jami'an ke yi na ceto wadanda suka makale cikin barakuzan ginin da kuma ke da sauran ransu. Wani babban jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce ma'aikatan agaji na ci gaba da aiki tukuru domin ganin an zakulo sauran mutanen da ke karkashin ginin.

Al'ummar jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriyar dai, ta tsinci kai cikin rudani sakamakon wannan ibtila'in. Koda a shekara ta 2019 ma dai an samu afkuwar irin wannan ibtila'in, inda wani dogon benen ya fada kan wata makaranta tare da kashe dalibai kimanin 20 da kuma jikkata wasu da dama. Hukumomi a Najeriyar na danganta yawaitar rushewar gine-gine da rashin bin tsarin gini da ma rashin ingancin aiki.