1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rupiah Banda zai tsaya takara

November 17, 2014

Tsohon shugaban kasar Zambiya Rupiah Banda, ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar inda za'a zabi wanda zai maye gurbin marigayi Michael Sata.

https://p.dw.com/p/1Doh1
Hoto: AP

Tuni dai mutane da dama suka soki wannan mataki na shi ya samu kakkausar murya ciki kuwa har da shugaban jam'iyarsa ta MMD Nevers Mumba. Shi dai Rupiah Banda ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekara ta 2011, ya kuma bayyana cewa jagororin jam'iyarsa ta MMD da ma 'yan majalisu da ke karkashin inuwar jam'iyar sun amince da takarar tasa da kuri'u 19 daga cikin 23, inda ya kara da cewa babu wani lokaci da ya ke da shi na gudanar da yakin neman zabe sai dai ya na kira ga dukkan mambobin jam'iyar ta MMD na gaskiya da su bada goyon bayansu ga wannan takara tasa.

MAwallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman