Amirka ta shirya kare Ukraine daga Rasha
February 5, 2022A wannan Asabar rundunar sojin da Amirka ta yi alkwarin turawa a gabashin Turai ta soma isa, inda tawagar farko ta sauka a kasar Poland, tawagar na daga cikin wadanda kungiyar tsaro ta NATO ta amince a tsugunar saboda irin barazanar da kungiyar ta ce, kasar Ukraine na fuskanta daga rundunar sojin Rasha.
Akalla sojoji dubu uku Amirka ta shirya aika wa yankin Gabashin Turan, don zama cikin shiri a mamayar da ake zargin mahukuntan Moscow da shirin yi wa Ukraine.
Baya ga wadannan sojojin da ake shirin jibgewa a kasashen da ke zagaye da Ukraine, manyan kasashen duniyan sun yi barazanar sanya wa Rasha takunkumi, muddun ta kuskura ta kai wa Ukraine hari, zargi ne da tuni Shugaba Vladimir Putin ya musanta, maimakon hakan ya zargesu da yunkurin tayar da zaune tsaye na kunna wutan rikicin yaki a tsakanin kasarsa da makwabciyarta.