1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar addini a Saudiyya na ƙara fuskantar koma baya

October 18, 2012

A cikin matakan sauye sauye da suke ɗauka humumomi a Saudiyya sun ƙara taƙaita ayyukan 'yan sandan addini a cikin ƙasar.

https://p.dw.com/p/16Ri8
Hoto: picture-alliance/dpa

Tun a ƙarni na 18 a ƙasar Saudiya aka kafa ƙungiyoyin dogarawan addini dake horo da aikin alheri da hani daga alfasha. Sannan a hukumance a shekarar 1819 waɗannan ƙungiyoyi suka zama wata hukumar rundunar 'yan sandan addini a ƙasar at Saudiya. Duk da rawar da suke takawa wajen ganin an bi dokokin shari'ar Musulunci masu tsauri da ƙasar ke aiki da su, yanzu haka hukumomin Saudiyan sun rage wa wannan runduna ƙarfin ikonta.

Babban malamin addinin Islama a Saudiya Muhammad ibn Abdal Wahab wanda ya yi rayuwa a ƙarni na 18 wanda kuma ƙasar ke bin koyarwarsa ta tsauraran dokokin addinin Musulunci ko kuma Wahabiyanci a wata fassarar, ya ba da muhimmanci wajen ganin al'umar ƙasar sun bi kyakkyawan tafarki a dukkan fannoni na rayuwa. Wannan na daga cikin dalilan da ya sanya aka ƙirƙiro da ƙungiyoyin kare addini a ciki da wajen birnin Makkah, waɗanda a shekarar 1918 a hukumance aka mayar da su rundunar 'yan sandan addini. A shekaru da suka biyo baya an yi ta ƙara musu iko.

Sai dai ikonsu ya dogara ga yanayin siyasa, wato idan masu ra'ayin mazan jiya ke da faɗa a ji, rundunar ta fi tsauri, amma idan masu matsakaicin ra'ayi ne a kan mulki, 'yan sandan na nuna sassauci. Yanzu haka dai yawansu ya kai 4500.

Guguwar sauyi ta kai ga Saudiyya 

Tun kimanin shekaru 10 da suka wuce gwamnatin Saudiya ta taƙaita ikon rundunar 'yan sandan addinin. Yayin da 'yan sandan addini suke da ikon kama wa da yi wa 'yan Saudiyya shari'a yanzu an janye wannan ikon an ba wa 'yan sandan farar hula. Hakan dai na da nasaba da sauye sauyen da ake samu a cikin ƙasar inji Menno Preuschaft masanin addini da siyasa.

"Kamar a sauran ƙasashen Larabarawa, ita ma Saudiyya tana fama da na ta matsaloli na zamantakewa. Akwai matasa da yawa dake fama da rashin aikin yi. Wannan babban ƙalubale ne ga ƙasar, domin ya na iya haddasa wani juyin juya hali cikin sauri. Kasancewa ƙasar tana da arzikin man fetir, tana da kuɗin rage kaifin wannan matsala."

Saɓani tsakanin 'yan gargajiya da masu rajin canji

Har yanzu dai akwai rashin jituwa tsakanin masu bin dadaɗɗun al'adu da masu neman sauyi. Yayin da wasu suka dage kan ci-gaba da bin dokokin musulunci tsantsa, a ɗaya ɓangaren ƙasar ne ƙoƙarin amfani da arzikin man fetir da sabunta kanta domin ta dace da zamani musamman a fannoni kimiyya da fasaha wanda ya sa ƙasar ta buɗe kofofinta ga sauran ƙasashen duniya.

Saudi Arabien Jugendliche Jubel Protest Symbolbild
Su ma matasa Saudiyya ba a bar su a baya ba wajen neman sauyiHoto: Getty Images

Sulaiman Addonia marubucin ƙasar Eritrea wanda tun yana yaro ƙarami a cikin shekarun 1980 ya je Saudiyya, amma ya bar ƙasar a shekarar 1990. A dangane da abubuwan da ya gani a Saudiya, a shekarar 2009 ya wallafa wani littafi mai taken "Sakamakon Soyayya" inda a ciki ya yi bayayi game da tarbiyya da zamantakewa a Saudiya.

"Kasancewa an harmata haɗuwar maza da mata a wuri ɗaya, ya sa rashin ɗaya jinsi ya janyo wani yanayi ba ma kaɗaita kaɗai ba, har da rashin ƙaunar wani abu a zucci."

A saboda haka matasa da yawa a Saudiyya ke bukatar a sakar musu mara don tafiyar da rayuwarsu yadda suke so. Sai dai har yanzu akwai dogon shinge a gabansu.

Mawallafa: Kersten Knipp / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe