1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rufe sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab

Linda Staude/Suleiman BabayoJune 27, 2016

Kenya tana shirin rufe sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya na Dadaab da ke kunshi da 'yan Somaliya wanda yake gabashin kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/1JEYS
Kenia Das Flüchtlingslager Dadaab
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya shi ne na Dadaab da ke gabashin Kenya, wanda ya kunshi 'yan Somaliya fiye da 320,000. An bude wannan sansani tun farkon shekarun 1990 lokacin da rikicin kasar Somaliya ya barke. Sai dai bayan tsawon lokaci yanzu sansanin na Dadaab ya fuskantar rufewa daga mahukuntan Kenya.

Mahukuntan Kenya da Somaliya gami da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalaisar Dinkin Duniya suka amince domin fara kwashe 'yan gudun hijira zuwa gida, saboda gwamnatin Kenya ta tsaya kai da fata tana neman rufe sansanin bisa dalilan musamman na tsaro.

Kenia Impfung Dadaab Flüchtlingslager
Hoto: Getty Images

Haka ya nuna tilas 'yan gudun hijira na Somaliya da ke Kenya za su koma gida ke nan. A kan wannan lamari babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Filipo Grandi ya gana da Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ta Kenya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar ta tabbatar da cewa wannan mayar da 'yan gudun hijira daga Kenya zuwa Somaliya na bisa radin kai ne ga wadanda suka amince. Abin da ministan harkokin wajen Somaliya Abdusalam Omer ya kara ba da tabbaci.

Wannan aikin zai gudana har zuwan ranar 30 ga watan Nowamba mai zuwa za a rufe wannan sansanin na 'yan gudun hijira baki daya wanda ya fi girma a duniya. Abdusalam Omer ministan harkokin wajen kasar ta Somaliya ya ce aikin zai gudana cikin tsari, kuma ya musanya masaniya kan lokacin da aka tanada.

A daya bangaren babban jami'in kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filipo Grandi ya ce ana saran zuwa karshen wannan shekara kimanin 'yan gudun hijira 150,000 za su koma Somaliya bisa radin kai. Haka kimanin rabin adadin 'yan gudun hijira da ke Dadaab ke nan. Amina Mohamed ministar harkokin wajen Kenya ta tabbatar da rashin tilasta wa mutane komawa gida amma ta ce akwai kalubale.

Kenia Dadaab, Somalische Flüchtlinge
Hoto: Getty Images

Kiyasi ya nuna rufe sansanin 'yan gudun hijira da ke Dabaab na kenya zai lakume kadaden da suka kai Euro milyan 200, inda ake sa ran samun kimanin Euro milyan 190 na daga masu ba da agaji na kasashen duniya.