1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka: Karfafa tsaron kan iyakoki

Zulaiha Abubakar
November 22, 2019

Kasar Girka za ta jibge jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana a kan iyakokinta, da nufin hana bakin haure kwarara cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/3TXwI
Griechenland l Ministerpräsident Kyriakos Mitsotakis
Hoto: picture alliance/AP Photo/P. Giannakouris

Firaministan kasar ta Girka Kyriakos Mitsotakis ne ya sanar da hakan yayin da yake  yi wa zauren majalisar dokokin kasar jawabi game da kutsen da sabon ayarin bakin haure suka yi cikin kasar ba bisa ka'ida ba.

Yanzu haka dai zauren majalisar ya amince da bukatar firaministan na baza jami'an tsaron da yawansu yakai 400, wadanda zasu yi aikin sintiri a kan iyakar kasar da Turkiyya da ke makwabtaka da kuma wasu dakaru 800 wadanda za su yi aikin tsaro a yankunan da ke da tsibiri, bayan inganta aikin shige da fice a tashosin ruwa. A ranar Larabar da ta gabatane  gwamnati ta sanar da shirinta na rufe sansanin 'yan gudun hijirar da ke yankin.