Rufe makarantu don illar gurbacewar mahalli
November 14, 2024Ministan kula da ilimi a yankin ya ce birnin New Delhi da kewaye duk an basu umarnin rufe makarantun furamare har sai abin da hali ya yi. Yankin mai kimanin mutane miliyan 30, ana kiyasin yara da dama na mutuwa sakamakon gurbacewar mahalli, don haka ne ya zama wajibi hukumomi su dauki matakin ceto rayukan yara. An dai sha samu dai-daikun makarantu na rufewa a babban birnin kasar ta Indiya sakamakon yadda birnin ke zama duhu wasu lokuta sakamakon hayakin da masana'antu da motoci ke haddasawa. A cewar masana wasu lokutan hadirin yahaki da ke rufe birnin baya ga wanda kamfanonin ke fitar wasu hayakin na fitowa ne daga kone-kunen tayoyi da masu share filayen gonaki a kewayen birnin mai cunkoson jama'a. Don haka ne a hukumance gwamnati ta dau matakin rufe makarantun furamare ta yadda za a kare yara da gurbataccen hayakin ke yi wa illah.