1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a kasar Masar

June 21, 2012

Hukumar zaben Masar ta sanar da dage sakamakon zaben shugaban kasar- abin da ka iya janyo sake shiga juyin juya hali

https://p.dw.com/p/15J7z
An Egyptian elections official holds unusable ballots at a polling center after the second day of the presidential runoff, in Cairo, Egypt, Sunday, June 17, 2012. As Egyptians voted in a second day of elections for a successor to Hosni Mubarak, the ruling military issued an interim constitution Sunday defining the new president's authorities, a move that sharpened the confrontation with the Muslim Brotherhood and showed how the generals will maintain the lion's share of power no matter who wins. The Arabic handwriting from top to bottom reads " revolution will continue, Hamdeen Sabahi, down with military rule, remnants of old regime, brotherhood." The Arabic in print reads "presidential runoff candidates 2012, Ahmed Shafiq, at top, and Mohammed Morsi. " (Foto:Amr Nabil/AP/dapd) // Eingestellt von wa
Hoto: dapd

An shiga wani rudani a Masar bayan da hukumar zaben kasar ta dage sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da ake jira a ranar Alhamis.

Hukumar zaben dai ta ce ta dage sanar da sakamakon har illa ma sha'allahu saboda duba korafe korafen da 'yan takarar biyu suka yi wadanda kowannensu ya ba da sanarwar cewa shi ya lashe zaben. Wannan sanarwa ta sanya yawancin 'yan kasar na sake gaskanta jita-jitar da ake na cewa tana fuskantar matsin lamba daga mahkuntan soji kasar da jami'an leken asiri kan ta murda sakamakon zaben da Mohammed Mursi ya kama hanyar lashewa don ta ba wa Ahmed Shafik.

Alkalan kasar da ke wa kasu kirarin tsimagiyar kan hanya fyadi yaro fyadi babba sun ce tarihin ba zai rgaa masu ba idan suka yi gum da bakinsu suna ganin ana shirin yin shedar zur -lamarin da ya sanya suka bayyana sakamakon zaben ga 'yan jaridu. Mohammed Mursi ya samu kuriu miliyan 13 da doriya, kana Ahmed Shafik ya samu miliyan 12 da dubban kuri'u . Don hakasMursi shi ne ke kan gaba da fifikon kuri'u har dubu 884.

Tsoron shiga yakin basasa

Kungiyoyi masu fafutuka da jam'iyyun siyasa da suka hada da 'Yan uwa Musulmi sun fara yin zaman dirshan na sai baba ta gani a dandalin Tahrir har sai an bayyana Mohammed Mursi a matsayin wanda a lashe zaben.

epa03271043 Supporters of Egypt's Muslim Brotherhood candidate Mohammed Mursi celebrate in Tahrir square after the announcement of the presidential elections results in Cairo, Egypt, 18 June 2012. Muslim Brotherhood claim that its candidate Mohammed Mursi had won an historic presidential election. In a statement Mursi said he would be a president for all Egyptians. Ahmed Sarhan, the campaign spokesman of Ahmed Shafik, Mubarak's last prime minister, also contending the presidential post, meanwhile said only about 40 per cent of the votes were counted, and accused the Mursi camp of manipulating the media. EPA/JULIEN WARNAND
Magoya bayan Mohammed MursiHoto: picture-alliance/dpa

" Wannan mataki wani makirci ne ake son kullawa. Mu kuwa a shirye muke mu ba da jininmu don kare zaben da muka yi . Me mahukuntan soji za su fada mana? Bayan mun rasa 'yan uwanwajen yin juyin juya hali amma a ce suna son su kawo mana nulkin kama karya?."

" Mohammed Mursi muna tare da kai. Muna nan daram har sai an zo an rantsar da kai a wannan dandali. Ba za mu amince da 'yan fashin zabe ba . Ya Mursi kar ka karaya ko ka saurari wasu 'yan baranda daga waje:"

Ita kuwa gamayyar matasan juyin-juya-hali wata takarda a fitar tana gargadin jefa kasar cikin yakin basasa matukar aka yi murdiya a sakamakon zaben.

Matsayin Amirka kan lamarin

Kasar Amirka da ta ce tana tsoron barkewar yamutsi a kasar matukar aka murda sakamakon ta nemi mahukuntan sojin kasar da su mutunta alkawarin da suka yi a aikace kamar yadda suke fadi a fatar baki. A ta bakin sakataren harkokin wajenta, Hilary Clinton kasar ta Amirka ta ce ta kadu da matakan baya bayan nan da mahukuntan sojin kasar suka dauka na rusa cibiyoyin dimokuradiyya da kuma jan kafa wajen bayyana sabon shugaba da 'yan kasar suka zaba.

U.S. Secretary of State Hillary Clinton talks during a presser with Egyptian foreign minister Ahmed Aboul Gheit, not pictured, following her meeting with President Hosni Mubarak at the Presidential palace in Cairo, Egypt, Wednesday, Nov. 4, 2009. Talks come within the framework of efforts aimed at reviving the Middle East peace process. (AP Photo/Amr Nabil)
Hillary ClintonHoto: AP

Idan dai har aka ce hukumar zaben kasar za ta duba takardun korafi har 440 kana ta dauki mataki kansu to zai yi wuya a ce an sanar da sunan shugaban kasar kafin nan da karshen watan Yuni - wa'adin da sojojin suka ce za su koma barikokinsu.

Za a a iya sauraron sautin wannnan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Mahmud Yahaya Azare
Edita: Halima Balaraba Abbas