1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Hanyar isar da sakon matasalolin mutane

June 16, 2021

Wani matashi a jihar Sokoto da ke Najeriya ya zabi ya soma aikin rubuce-rubuce don zakulo matsalolin da ke damun al'umma ya isar da su ta hanyar rubutu ko faya-fayan bidiyo.

https://p.dw.com/p/3v2hz
Buchstaben Spielzeug
Hoto: Colourbox

Wani matashi a jihar Sokoto da ke Najeriya da ya kammala digirin sa a fannin kimiyar siyasa ya zabi ya soma aikin rubuce-rubuce don zakulo matsalolin da ke damun al'umma ya isar dasu ta hanyar rubutu ko faya-fayan Video da manufar shugabanni su gani don magance matsalolin.

Shi dai wannan matashi mai cikakken suna Abdulmumin Lawal Mande da akafi sani accidental poet ta bangaren rubuce-rubucen sa, yace ya shafe sama da shekaru hudu zuwa biyar yana gudanar da wannan rubuce-rubuce musamman ma wajen zakulo matsalolin dake damun al'umma ya kuma bayyana su ta hanyara rubutu. Matashin Abdul yayi bayanin yadda karon farko abunda ya ja hankalin sa har ya tsinci kansa cikin wannan aikin rubuce-rubuce

Koda yake matashi Abdul ya bayyana irin kalubale da kuma nasarori dake tattare a cikin wannan rubuce-rubuce da ya shafe dogon lokaci yana  gudanarwa. Matashin dai yace yanzu haka yana horar da matasa dubarun salon rubuta  don su fahimci sanin yadda zasu isar da sako ta hanyar alkalami.