1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: Rishi Sunak ya samu gurbin shiga takara

Abdoulaye Mamane Amadou
October 22, 2022

A kokarin maye gurbin firaminista a Birtaniya, tsohon sakataren kudi Rishi Sunak ya tattara adadin kuri'un da ke bashi damar shiga takara a jam'iyya Conservative duk da hasashen takarar Boris Johnson

https://p.dw.com/p/4IXjI
Tsohon firaminista Boris Johnson da tsohon sakataren kudi Rishi Sunak
Tsohon firaminista Boris Johnson da tsohon sakataren kudi Rishi SunakHoto: Andrew Parsons/Photoshot/picture alliance

Tsohon sakatare kudin Biratniya Rishi Sunak ya bayyana samu sahalewar membobin jami'yyar Conservative ta Birtaniya fiye da 100 da ka ba shi cikakkiyar dama ta tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar domin maye gurbin firaministar kasar  Liz Truss da ta yi bankwana daga kujerrar mulki a tsakiyar mako.

Tuni ma dai wasu daga cikin magoya bayan dan takara Rishi Sunak da ya sha kaye a zaben maye gurbin Boris Johnson da Liz Truss a farkon watan jiya suka fara bayyana goyon bayansa a shafukansu na sada zumunta.

Ana hasashen tsohon firaministan Birtaniya da ya yi marabus bayan matsin lambar da ya fuskanta Boris Johnson na da sha'awar yin kome kan takarar mukamin. A ka'idance sai kowane dan takara ya samu amincewar 'yan majalisun dokokin jam'iyyar ta Conservative 100 daga cikin fiye da 300 kafin nan ya shiga jerin 'yan takarar shugabancin jam'iyyar, kana daga bisani magoya bayan jam'iyyar su amince da kada masa kuri'ar cancanta ko akasin haka.