1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rincabewar al'amura a kasar Sudan

April 17, 2023

Rahotanni daga Sudan na cewa ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin gwamnati da mayakan kungiyar tsaro ta ko ta kwana RSF a Khartoum babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4QCpp
Hoto: Marwan Ali/AP/picture alliance

Har kawo yanzu babu bangare da ya yi nasara a fadan mai kama da yunkurin juyin mulki da aka fara gwabzawa tun a ranar Asabar, wanda kuma kawo yanzu ya yi ajalin mutane 97 ciki har da jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya uku a alkalumn da kungiyar likitocin kasar ta fitar a safiyar Litinin.

Masu aiko da rahotannin sun ce gumurzun daren jiya ya yi zafi sossai a birnin inda aka yi ta jin karar manyan bindigogi da hare-hare na jiragen yaki, yayin da aka shiga kwana na biyu na rashin wutar lantarki da ruwa sha a wasu unguwannin birnin Khartoum.

Kungiyoyin kasa da kasa dai na ci gaba da kiran bangarorin gwamnatin Sudan da tsoffin mayakan na RSF da su ajiye makamai, sannan kuma  kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar kasashen Labarawa sun kira tarukan gaggawa tare da sanar da aike Mousa Faki Mahamat domin shiga tsakani.

Haka ma kungiyoyin yankunan biyu, na bukatar da a tsagaita bude wuta domin ganin yadda za a yi wa tufkar hanci tun kafin lamarin ya kai ga gagarar kundila.

Al'umma a kasar dai na ci gaba da nuna fushinsu tun bayan hambarar da mulkin farar hula da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoban shekarar 2021.

Kawunan 'yan kasar ta Sudan na a rarrabe, a yayin da wasu ke kin amincewa da matakin sojojin, a karshen makon da ya gabata daruruwan masu goyon bayan sojojin sun gudanar da ta su zanga-zangar.