1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin zabe ya bar baya da kura

January 8, 2021

Majalisar Dinki Duniya ta ce mutane fiye da dubu 30 ne rikicin zabe ya tilasatawa barin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yayin da wasu dubbai ke gudun hijira.

https://p.dw.com/p/3ni0m
Afrika Menschen fliehen vor Gewalt in Zentralafrika
Hoto: David Belluz/AP Photo/picture alliance

Hukumar Tallafa wa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda suka bar kasar Afirka ta Tsakiya zuwa kasashe makwafta na neman agajin gaggawa na ruwa da abinci da matsugunni da kuma kiwon lafiya. Hukumar zaben kasar dai ta bai wa shugaba mai ci Faustin Touadera a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar Litinin sai dai 'yan adawar kasar sun yi kira da a soke zaben saboda zargin tafka kura-kurai.Jamhuriyar Afirka ta tsakiya dai na daga ciki kasashen da ke fama da talauci a duniya kuma ta fuskanci jerin juiyn mulki da yake-yake tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.