Rikicin yankingabas ta tsakiya
November 13, 2006Talla
Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da suka hadar dana yankin Palasdinawa ,sunyi kira da a kaddamar da wani taro na musamman adangane da sabon tsari na wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,wanda zai samu halartabn manyan kasashe masu fada aji na mdd da wakilan larabawa da Izraela.Bugu da kari ´ministocin a wani taron gaggawa da suka gudanar a birnin Alkhahira,sun yi alkawarin kawo karshebn takunkumin tallafin kudade da aka dorawa yankin palasdinawa ,sakamakon nasaran da yan hamas suka samu a zaben watan janairu.Ministocin larabawan sun bayyana muradinsu na bawa hukumar palasdinu tallafi ,ba tare da laakari da manufofin Amurka dana sauran kasashen turai ba,inji babban sakataren kungiyar kasashen Amr Moussa.