1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin 'yan dabar kasar Haiti ya raba mutane da gidajensu

Binta Aliyu Zurmi
October 2, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 700,000 ne rikicin 'yan dabar kasar Haiti ya raba da matsugunnensu.

https://p.dw.com/p/4lLTA
Mexiko schickt weitere 130 Migranten nach Haiti
Hoto: Daniel Becerril/REUTERS

Hukumar kula da kaurar jama'a ta majalisar ta ce daga farkon watan Satumba da ya gabata mutane 702,897 ne rikice-rikicen 'yan daba ya tilastawa tsrewa daga matsugunnensu wanda ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

A cewar hukumar mafi akasarin wadannan wannan matsalar ta fi shafa mata ne da yara kanana.

Kasar Haiti wace ke zama guda daga cikin kasashen duniya da ke fama da matsanancin talauci, rikicin ya jefa ta shiga wani hali, inda ta kai ga 'yan daba kwace iko da Port-au-Prince, babban birnin kasar da mayar da jami'an tsaro karkashin ikonsu gami da rugujewar ma'aikatar lafiya.

Matsalar tsaro a kasar ta yi kamarin da mahukunta neman agaji daga kasashen duniya. 

Karin bayani:Rukuni na biyu na 'yan sandan Kenya na shirin zuwa Haiti