1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfin dangantakar Rasha da Afirka

March 9, 2022

Rasha ta dade ta na fadada tasirinta a Afirka tsawon shekaru da dama. Wannan ya kara bayyana a dambarwar diflomasiyyar da aka shiga a yanzu bayan harin da ta kaddamar kan Ukraine.

https://p.dw.com/p/48EYm
Rasha I Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Faustin Archange Touadera tare da Vladimir Putin
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera da Vladimir PutinHoto: Sergei Chirikov/AP Photo/picture alliance

A ranar biyu ga wannan wata na Maris da muke ciki, babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York ya bukaci kada kuri'a a kan Rasha ta gaggauta janyewa daga Ukraine ba tare da wani sharadi ba. Yawancin kasashen sun kada kuri'unsu, inda kasashe 141 suka kada kuri'ar amincewa. A lokacin kada kuri'ar abu guda ya fito karara, kasashen Afirka sun rarrabu a kan batun Ukraine din, saboda kasashe 25 sun kauracewa kada kuri'ar. Iritiriya ta fito karara ta kada kuri'ar kin amincewa da daftarin. Kasashen Kamaru da Habasha da Guinea da Guinea Bissau da Burkina Faso da Togo da Eswatini da Moroko kuwa, sun yanke shawarar yin rowar kuri'unsu ne.

Karin Bayani: Turkiyya ta taimaki Ukraine da kayan yaki

Kasashen Aljeriya da Yuganda da Burundi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali da Senegal da Equatorial Guinea da Kwango da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Sudan da Sudan ta Kudu da Madagaska da Mozambik da Angola da Namibiya da Zimbabuwe da kuma Afirka ta kudu kuwa, sun kauracewa kada kuri'ar kan batun mamayar Rashan ne. A kasar Afirka ta Kudu musamman 'yan boko da jami'an diflomasiyya da 'yan siyasa na bangaren adawa, sun soki lamirin matakin da gwamnatin ta dauka. Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya kare matsayin gwamnatinsa na zama 'yar ba ruwanmu, hasali ma ya zargi kasashen yammacin Turai ne da rashin yin kokari sosai wajen sasanta rikicin tsakanin Rasha da Ukraine.

Ukraine Donetsk | Hare-Haren Rasha
Hare-haren sojojin Rasha, na ci gaba da tarwatsa gine-gine a UkraineHoto: Leon Klein/AA/picture alliance

A cewar wani masanin kimiyyar siyasa na kasar Angola Olivio N'Kilumbu yawancin 'yan jam'iyyar ANC ta Afirka ta Kudu da ke mulki a kasar tun zamanin wariyar launin fata, suna goyon bayan Rasha ne. Masanin kimiyyar siyasar N'Kilumbu ya ce Rasha ta ci gaba da yada angizonta a kan kasashen da Tarayyar Soviet ta taimakawa, kasashe kamar Angola da Mozambik da Zimbabuwe da kuma Namibiya, yana mai cewa a lokacin yakin wariyar launin fata Tarayyar Soviet ta taimakawa kungiyoyin gwagwarmayar kwatar 'yanci kamar MPLA da FRELIMO da ZANU da kuma SWAPO da tarin makamai da kuma horon soja.  A 'yan shekarun baya-bayan nan gwamnatin Rasha ta tuna da kasashen da Tarayyar Soviet ta taimaka musu, ta kuma ci gaba da fadada alaka da su ta fannin siyasa da tattalin arziki da kuma dangantakar soja.

Karin Bayani: 'Yan Najeriya sun fara isa gida daga Ukraine

A shekarar 2019, Vladimir Putin ya dauki bakuncin taron kolin Rasha da Afirka da ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka 43. Babu ma kuma inda dangantakar Afirka da Rasha ta fi karfi kamar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, haka ma kuma Rasha ta fadada tasirinta a Mali mai fama da rikici a baya-bayan nan. Tierno Monenembo wani marubuci na kasar Guine ya yi tsokaci yana mai cewa, a irin wannan yanayi yana da matukar wuya kasashen Afirka su dauki matsayi. Ya nunar da cewa idan kana karami kuma ya kasance kana da rauni sannan ba ka da karfin makamai kuma ga rashin ci-gaba, ba za ka yi azarbabin shiga cikin rigimar kasashe masu karfin makamai ba.