1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta ja hankalin jaridu

Usman Shehu Usman ZMA
December 3, 2021

Jaridun sun yi nazarin rikicin da ya ritsa da dakarun Faransa a Nijar da zanga zangar Burkina Faso da kuma halin da ake ciki a Kongo da sabon nau'in corona na Omicron.

https://p.dw.com/p/43oet
Afrika | Burkina Faso | Soldaten im Einsatz in Bobo-Dioulasso
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/D. White

Cikin shirin sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka zamu fara da Jamhuriyar Nijar. Inda jaridar die tageszeitung,ta fara da aza ayar tambaya, wai shin wa ya yi harbi a Téra na jamhuriyar Nijar? Ta ce Babban tashin hankali dai ya faru a Téra, birni mai mazauna akalla 90.000 a yankin Kudu maso Yammacin Nijar.

Lamarin ya faru ne lokacin da wani ayarin sojojin Faransa suka biyo ta jamhuriyar Nijar kan hanyarsu zuwa Mali. Sojojin na Faransa na samun rakiyar jandarmomin kasar Nijar kimanin  40, wasu mutane biyu sun mutu biyu. A bangarensa shugaban kasar Mohamed Bazoum, ya kafa kwamiti nan take da zai binciki ainihin abin da ya faru.

Jaridun Jamus
Jaridun JamusHoto: imago/Future Image

Daga jamhuriyar Nijar za mu tsallaka izuwa makwabciyarta Burkina Faso, inda jaridar Neues Deutschland, ta yi labarinta kan boren kin jinin gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore. Jaridar ta ce wasu 'yan kasar Burkina Faso sun fara gajiya, suna ganin an kyalesu ba mai kula da rayuwarsu yayin da mayakan jihadi suka addabesu da hare-hare.

Kungiyoyin fafutuka, jam'iyyun adawa da sauransu ne dai suka yi kiran a yi zanga-zanga a fadin kasar don neman shugaba Kabore ya sauka daga mulki. A Ouagadougou babban birnin kasar, jami'an tsaron sun killace wasu titunan sun kuma harba hayaki mai sa kwalla kan masu boren. Babban dai abin da ya fi daga hankalin 'yan kasar ta Burkina Faso, shi ne harin ta‘addanci da aka kai a ranar 22 ga watannan, inda mutane 19 suka mutu.

Sojojin kasar Burkina Faso
Sojojin kasar Burkina FasoHoto: Imago Images/ZUMA Press/D. White

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi sharhinta ne kan sabon nau'in annobar corona wato Omicron. Ta ce wai shin tsauraran matakan hana tafiye-tafiye zai magance yaduwar cutar, shin hakan yana da sauki ne? Jaridar ta kara da cewa masanan kimiyar dai sun ce a yanzu wannan sabon nau'in Omicron shi ne abu mai hatsari.

To amma a baya an samu wasu nau'o'in, a bayan an dau tsauran matakai na hana zirga-zirga kusan a fadin duniya, wancan lokacin kasar Afirka ta kudu na cikin wadanda suka fi jin radadin matakan, kuma a yanzu ma kasar za ta fiskanci wani zagayen jin jiki bisa matakan da duniya ke dauka na hana zirga zirga zuwa ko fitowa daga kasar.

Alluran rigakafin corona
Alluran rigakafin coronaHoto: Andre M. Chang/Zuma/picture alliance

Kotu za ta binciki Joseph Kabila. Wannan shi ne labarin Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce a kasar da harkoki suka wargaje cikin shekaru masu yawa, wato Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, yanzu an fara tattara takardun tuhumar yadda tsohon shugaban kasar ya yi rub da ciki da kudin baitil malin gwamnati. Binciken da aka fara kimanin mako guda, an yi masa lakabin "Fashi da makami wa Kongo" kamar yadda kafafen yada labaran duniya da kungiyoyi masu zaman kansu suka dade suna bada labarin irin yadda tsohon shugaba Joseph Kabila, da iyalansa hadi da mukarrabansa na siyasa, suka yi ta diban kudin daga aljihun gwamnati.