1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan ta kudu da ta arewa na karuwa

Usman ShehuJanuary 3, 2013

Sudan ta kudu ta zargin dakarun Khartum da kai harin bama-bamai kan iyakar da kasashen biyu suke takaddama

https://p.dw.com/p/17DPI

Hukumomi a Sudan ta kudu, sun zargi dakarun gwamnatin Sudan ta da kai harin bama-bamai a kan iyakar da kasashen biyu ke takaddama a kanta. Hakan ya farune sa'o'i gabanin gawanar shugabannin kasashen biyu. Ba a dai samu damatr jin ta bakin sojojin gwamnati a Khartum ba, don mayar da martani.

Ana dai saran shugaban Umar Albashir na Sudan, zai gana da takwaransa na Sudan ta kudu Silva Kiir a birnin Adis-Ababa gobe Jumma'a idan Allah ya kaimu. A watan Satumban bara shugabannin biyu suka sa hannu kan zaman lafiya da ya kai ga warware matsaliloin dake tsakaninsu, inda Sudan ta kudu ta amince ta sake ci gaba da tuno mai. Man da Sudan ta kudu ke tonowa dai butunsa sun bi cikin Sudan ta arewa ne, inda dukkan bangarorin biyu ke amfana da albarkatun man.

Daga bisani Sudan ta kudu ta dakatar da tono man, inda tace Sudan ta arewa na sace man. Ana saran Firimiyan Habasha Hailemariam Desalegn, tare da wakilin kungiyar AU a tattaunawar kasashen wat,o Tabo Mbeki za su matsawa shugabannin biyu don cimma matsaya.