1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Yara kimanin 1,200 suka halaka a rikicin Sudan

Suleiman Babayo AMA
September 19, 2023

Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin bangarorin da ke rikici a Sudan kiyasi ya nuna yakin na ci gaba da lakume rayukan yara sakamakon annobar da aka samu.

https://p.dw.com/p/4WZ9v
Sudan hayaki na tashi a birnin Khartoum
SudanHoto: Wang Hao/XinHua/picture alliance

Yara kimanin 1,200 suka halaka a sansanonin 'yan gudun hijra na kasar Sudan tsakanin watan Mayu zuwa wannan wata na Satumba bayan barkewar rikicin da ke ci gaba da tarwatsa kasar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce annobar cutuka irin kyanda da rashin abinci suka janyo mutuwar yara yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin bangarorin, kuma akwai yuwuwar samun karin dubban yara da za su halaka muddun aka gaza daukar matakan magance yayin da kasar ta Sudan ta samu kanta na yaki tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna.