1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan na ci gaba da tayar da hankali

April 27, 2023

Sudan ta shiga cikin rudanin siyasa, sakamakon takaddamar da ta fito fili tsakanin manyan jagororin gwamnatin kasar. Wannan matsala dai ba ta tsaya ga ita Sudan din ba a yanzu.

https://p.dw.com/p/4Qdu0
Hoto: Etat Major Des Armees/abaca/picture alliance

Babban abinda ya zame abin damuwa a Sudan tun bayan tashin hankalin da ya barke kusan makonni biyu, shi ne rashin girmama yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke gaba da juna. Kasar Amirka ce ta shiga tsakani domin neman an tsagaita wutar, akalla saboda samar da agajin jinkai da kuma bai wa kasashe damar kwashe mutanensu da ke makale a cikin rikicin. 

Yanzu dai akwai dubban 'yan kasar Sudan din da suka gudu zuwa kasashe makwabta domin tsere wa hare-haren da ake kai wa juna a kasar tasu. Baya ma ga 'yan Sudan din mai dai akwai wasu bakin da dama ke a kasar da su ma suka yi nasarar kubucewa zuwa makwabtan kasashen.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna