Rikicin Sudan da Sudan ta Kudu
April 25, 2012A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta AU ta ce ya zama wajibi Sudan da Sudan ta Kudun su janye dakarunsu daga yankin Heglig wanda ƙasashen biyu ke taƙaddama a kansa inda ta ƙara da cewa ko wacce ƙasa ta tabbata dakarunta na cikin ƙasarta sabanin zamansu a yankin na Heglig, sannan ƙungiyar ta yi kira garesu da su kawo ƙarshen faɗan da ake yi a Abiye da ma dai amincewa da iyakar da ke tsakanin ƙasashen kamar dai yadda Ramtane Lamamra ya shaidawa manema labarai bayan kammala wani taro da ƙungiyar ta AU ta yi cikin daren jiya.
Baya ga haka, ƙungiyar ta AU ta umarci mahukuntan Sudan da Sudan ta Kudu da su gujewa yin wasu kalamai da ka iya dagula dangantakar da ke akwai tsakaninsu da ma dai sake duba matsayin 'yan ƙasashen biyu da ba su zaune a ɓangarorinsu na asali.
Wannan umarni dai na zuwa ne daidai lokacin da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi ƙorafin cewar Shugaba Umar Hassan al-Bashir na Sudan ya bayyana cewar ƙasarsa ta shiga yaƙi da Sudan ta Kudu, a daidai lokacin da shi shugaba Kiir ke wata ziyara a ƙasar Sin wadda yanzu haka ya katse ta saboda halin da ƙasar ta sa ke ciki.
Ƙasar Sin na iya taimakawa wajen warware rikicin ƙasashen
To baya ga Ƙungiyar AU da ke son ganin ƙasashen biyu sun shiga tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu, yunƙurin da ƙasashen duniya su ka yi na'am da shi, a gefe guda ana ganin Ƙasar Sin wadda ke da dangantaka ta ƙut da ƙut da Sudan da Sudan ta Kudu na iya bada gudummawa wajen ganin ɓangarorin biyu sun warware matsalarsu cikin laluma kamar yadda Dick Agudah wani masani kuma mai sharhi kan ƙasahen biyu ya bayyana.
Mr. Agudah ya ce ''ƙasar Sin zata iya bada gagarumar gudummawa tare da taimakon Majalisar Ɗinkin Duniya domin kuwa ba za ta so a ce rikicin da ke tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ya bata danganta tsakaninsu ba''.
Gaza samun mafita ka iya yin awon gaba da kujerar Salva Kiir
Duk da cewar ana ganin za a iya samun mafita kan wannan matsala da ke tsakanin ƙasahen na Sudan da Sudan ta Kudu, masharhanta na ganin idan aka kasa cimma daidaito lamarin ba zai haifawa ƙasashen biyu ɗa mai idanu ba musamman ma dai shugaba Salva Kiir domin a cewar Agina Ojwang rikicin ka iya yin awon gaba da kujera shi shugaba Kiir ɗin musamman ma dai idan dakarun ƙasar ta sa su ka ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce.
Mr. Ojwang ya ce ''Sudan ta Kudu ba za ta iya ɗaukar irin luguden bama-baman da sojojin saman ƙasar Sudan za su yi mata ba saboda ƙasar ba ta da wadatattun kayan more rayuwa. Idan ko Sudan ɗin ta cigaba da yin hakan na tsawon lokaci kuma hakan ya cigaba da nakasa sojin Sudan ta Kudu to ko shakka babu dakarun Sudan ta Kudun na iya yin tunanin kawar da shugaba Kiir da maye gurbinsa da wanda su ke ganin zai iyan hawa teburin sulhu da mahukuntan Khartoum.
Shelar sakin fursunonin yaƙin da Sudan ta Kudu ta yi
Yayin da ake ƙoƙarin warware rikin na Sudan da Sudan ta Kudu, a gefe guda kuma da safiyar yau ne mahukuntan Sudan ta Kuda su ka yi shelar sakin fursosnin yaƙin da su ka kama yayin tada ƙayar bayan da aka yi yankin na Heglig a 'yan kwanakin da su ka gabata.
Da ya ke wa manema labarai ƙarin haske game da hakan, mai magana da yawun mahukuntan na Juba Barnaba Marial Benjamin ya bayyana cewar za su mika fursunonin yaƙin da su kama a gaban jami'an diplomasiyyar ƙasar Masar sai dai ya koka game da kunnen uwar shegun da ƙasar Sudan ta yi game da makomar sojojin Sudan ta Kudu da su ka kame wanda yawansu ya kai shidda, inda ya yi kira ga mahukuntan Khartoum da su yi biyyayya ga ƙa'idojin da dokokin ƙasa da ƙasa su ka shimfiɗa na ganawa da fursunonin yaƙi da ma sanin makomarsu in har su na raye.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe