1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Somaliya da matsalar 'yan gudun hijirar Afirka

September 11, 2015

Rikicin mayakan Al-Shabaab a Somaliya da taron kungiyar OECD kan Afirka a Berlin da matsalar 'yan gudun hijirar Afirka a Turai.

https://p.dw.com/p/1GVAO
Somalia Angriff auf African Union Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/M. Abdiwahab

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus a wannan makon ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Somaliya tana mai cewa mayakan Al-Shabaab suna dannawa inda ta kara da cewa 'yan tarzomar masu kaifin kishin addini suna kusa da Mogadishu babban birnin kasar.

Jaridar ta ce watanni biyu da suka wuce sun kasance munana ga sojojin rundunar Amisom da aka girke a Somaliya, inda ta yi asarar sojoji fiye da 60 a hare-haren da sojojin sa kai na Al-Shabaab suka kai. Jaridar ta ce abu mafi muni ba shi ne yawan sojojin da aka halaka, sai fa irin karfi da dubarun yakin da Al-Shabaab din ke da su na iya kai wadannan hare-hare wanda sai kwararrun sojojin kundunbala ne aka sani da wannan karfi. Shekaru hudu bayan nasarar da rundunar ta Amisom ta samu kan Al-Shabaab yanzu sojoji dubu 22 na rundunar sun koma kare kansu. Ganin wannan halin rashin tabbas da tashe-tashen hankula da kasar ta fada ciki, jaridar ta saka ayar tambaya ko za a iya gudanar da zabe kasar badi kamar yadda aka tsara?

Tallafa wa 'yan gudun hijirar Eritrea a Italiya

Taimako daga sama inji jaridar Die Tageszeitung inda ta kara da cewa: yanzu haka 'yan gudun hijira daga kasar Eritrea ne suka samu mafaka a cibiyar Baobab da ke birnin Roma na kasar Italiya, inda daidaikun mutane ke tallafa musu, amma daga bangaren hukuma babu wani taimako. Shi ma Paparoma Francis na daga cikin jerin wadanda ke ba wa 'yan gudun hijirar daga Afirka taimako. A cikin yini guda akalla 'yan gudun hijira 400 ne daukaci daga kasar ta Eritrea suka samu mafaka a cibiyar ta Baobab, wadda bisa ka'ida ya kamata ta dauki mutane 150 ne kawai. Sai dai a wannan lokaci na bazara a Turai dubban mutane ne musamman daga Eritrea ke neman mafaka a cibiyar da kungiyoyi masu zaman kansu ke daukar nauyin tafiyar da ita.

Flüchtlingscamp Calais
'Yan gudun hijirar Afirka a TuraiHoto: DW/L. Scholtyssek

Tallata nahiyar Afirka ga masu zuba jari

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan mako labari ta buga game da babban taron Afirka da kungiyar nan ta hadin kan tattalin arziki da raya kasa wato OECD ta shirya ranar Laraba a birnin Berlin, taron da jaridar ta kwatanta shi da tallata nahiyar Afirka.

Ghana Präsident John Dramani Mahama
Shugaba John Mahama na Ghana na daga cikin mahalarta taron na birnin BerlinHoto: BDI/C. Kruppa

Ta ce shin Afirka nahiya ce ta rikice-rikice ko kuma nahiya ce mai tattare da damarmaki? Dubi da kwararar 'yan gudun hijira a wannan lokacin inda 'yan Afirka ke da kashi daya cikin biyar, ana iya cewa Afirka nahiya ce mai fama da matsaloli. Sai dai idan aka yi wa lamarin karatun ta natsu, za a ga cewa da yawa daga cikin 'yan Afirka na da kkyakkyawan fata ga nahiyar duk da yake-yake na basasa da kuma radadin sauyin yanayi a nahiyar ta Afirka. Ko da yake a jawabinsa ga taron shugaban Ghana John Dramani Mahama ya ce wajibi ne a yi duk abin da za a iya na magance dalilan da ke sa 'yan Afirka musamman matasa ke daukar kasada yin hijira, amma bai yi karin bayani ga matakan da ya kamata a dauka bisa wannan manufa ba.