1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Gwamnatin hadaka ta Jam'iyyu uku ta rushe

Sabine Kinkartz ATB
November 7, 2024

Olaf Scholz ya kori ministan kudi na Jam'iyyar FDP. Bambancin siyasar da ke tsakaninsu. Olaf Scholz na so ya bukaci majalisar dokoki ta Bundestag domin kada kuri'ar amanna a tsakiyar watan Janairu.

https://p.dw.com/p/4mkkR
Hoto: Carsten Koall/dpa/picture alliance

 Gwamnatin hadakar Jamus ta Jam'iyyu uku ta rushe sakamakon rashin jituwa da zargin bita da kulli bayan da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na jam'iyyar Social Democrats SPD ya kori ministansa na kudi Christian Linder kuma shugaban Jam'iyyar FDPJam'iyun uku sun dade suna takaddama da juna kusan tun bayan da suka amince da tafiya tare su kafa gwamnati, sai dai abin da ya kai ga wannan hali shi ne takaddama kan yadda za cike wagegen gibi a kasafin kudin shekara mai zuwa da aka kasa cimma jituwa akai. Da yake tsokaci shugaban gwamnati Olaf Scholz ya ce sau da dama ya sha nuna alama ta yakana ina kau da kai amma sai Linder ya fito bainar jama'a ya mayar da lamarin wata takaddama tare da neman wasu bukatu na akida. Ya ce sau da dama Minister Lindner yana kare dokokin da ba su da muhimmanci.  Sau da dama yana amfani da wasu dabaru na siyasa ya ci amanarsa.  Ya ce wadannan al'amura a matsayin shugaban gwamnati sun kai matsayin da ba zai iya cigaba da jurewa ba.

Olaf Scholz da Christian Lindner ministan kudi
Olaf Scholz da Christian Lindner ministan kudiHoto: CHRISTOF STACHE/AFP

"Na nemi izini daga shugaban kasa domin sallamar ministan kudi. Dole ce ta sa na dauki wannan mataki domin kare kasarmu daga dukrkushewa. Muna bukatar gwamnati da za ta iya daukar mataki a lokacin da ya dace, wadda ke da karfin tasiri wajen yi wa kasarmu kyakkyawan jagoranci. Wannan shi ne abin da na bukata a shekaru ukun da suka gabata kuma shi ne abin da na ke bukata a yanzu. Tun da farko a yau na  yi wa Jam'iyyar Free  Democrats tayi managarci domin mu toshe gibin da ake samu a kasafin kudi don mu kauce jefa kasarmu cikin rudani".

Berlin Ende der Ampel-Regierung | Kanzler Scholz entlässt Lindner
Hoto: ODD ANDERSEN/AFP/Getty Images

A nasa bangaren Lindner ya zargi shugaban gwamnati Scholz da kokarin tilasta masa kau da kai daga abin da kundin tsarin mulki ya tanadar na iyakancewar bashi. Sai dai a daya gefen Jam'iyar SPD da kuma Jam'iyyar the Greens da ke cikin gwamnatin karkashin jagorancin Ministan tattalin arziki Robert Habeck da Ministar harkokin waje Annalena Baerbock sun zargi FDP da rashin nuna sassauci kan abin da suka ce na iya zama kasafin gaggawa, don samar da karin kudade. Jam'iyyun adawa sun yi amfani da wannan dama wajen kira ga shugaban gwamnatin Olaf Scholz da ya bukaci majalisa ta kada kuri'ar amanna a kuma yi shi da gaggawa fiye da yadda shugaban gwamnatin ya bukata.

Christian Lindner ministan kudi na Jamus
Christian Lindner ministan kudi na JamusHoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP

Jam'iyyun adawa na kawancen CDU da CSU sun ce ba za su lamunci gwamnati ta marasa rinjaye ba matukar shugaban gwamnati Scholz bai kira kuri'ar 'yan majalisa ba wanda ya ce yana fatan za a yi a cikin watan Janairu.Wannan dambarwa dai za ta dakatar da al'amuran gwamnati na tsawon makonni a wannan lokaci mawuyaci lamarin da fadar gwamnatin ba za ta so hakan ba. Ana sa ran Jagoran adawa Merz da shugaban gwamnati Scholz za su gana nan  gaba .