Rikicin siyasa a Masar
July 10, 2012A yaune ake saran majalisar dokokin ƙasar Masar za ta koma zamanta, bayan da sabon shugaban ƙasar Muhammed Mursi ya yi watsi da hukuncin kutu, kana ya umarci majalisar da ta koma aikinta. To amma kotun tsarin mulkin ƙasar a jiya ya sake jadda matsayinsa, inda yace hukuncin da ya yanke na rusa majalisar na nan daram. Ƙungiyar alƙalan Masar ta baiwa shugaba Mursi wa'adin sa'o'i 36 da ya soke matakin na sa, ko kuma ya gamu da fishinsu, haka dai su ma sojojin da suka mulki ƙasar ta Masar kafin zaben Mursi, sun aika masa irin wannan gargadin. Manyan janar din sojan Masar sukace za su ci gaba da kare kundin tsarin mulkin ƙasar. A watan jiyane kotu ta soke halarcin majalisa, daga bisani sojojin suka rusata dungurungum.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu