1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya ya yi ƙamari

February 14, 2012

Gwamnatin Siriya ta yi watsi da ƙudurin Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa na girka rundunar shiga tsakani

https://p.dw.com/p/1438J
Dies ist ein BILDAUSSCHNITT, das komplette Bild ist ebenfalls im CMS! In this undated image provided by ABC, Syrian President Bashar Al-Assad poses with ABC News Anchor Barbara Walters for an interview airing Wednesday, Dec. 7, 2011, on ABC. Assad denied he ordered the deadly crackdown on a nearly 9-month-old uprising in his country, claiming he is not in charge of the troops behind the assault. Speaking to Walters in a rare interview that aired Wednesday, he maintained he did not give any commands "to kill or be brutal." (Foto:ABC, Rob Wallace/AP/dapd)
Hoto: dapd

Dakarun dake biyyaya ga gwamnatin Siriya na ci gaba da lugudan wuta a birnin Homs dake matsayin sansanin 'yan tawaye.Hare-haren sun ƙara ƙamari bayan da gwamnati ta yi watsi da shirin Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa na girka rundunar shiga tsakani ta mussamman da zata ƙunshi sojojin ƙasashen larabawa da na Majalisar Ɗinkin Duniya.A wani rahoto da ta gabatarwa Majalisar Ɗinkin Duniya shugabar hukumar kare haƙƙoƙin bani adama Navi Pillay ta bayyana aniyar shigar da ƙaran shugaba Bashar Al-Assad na Siriya a kotun ƙasa da ƙasa,tare da tuhumar sa da aikata kisan kiyasu,ta kuma yi ƙarin haske ta na mai cewa:watani 11 kenan Gwamnatin na hallaka masu zanga-zangar neman 'yanci.Bamu da cikkaken bayani na yawan mutanen da suka rasa rayuka saboda bamu izinin shiga cikin ƙasar.Abinda ke tabbas shine kullum yawan mutane da ke rasa rayuka na ƙaruwa.

A cewar rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya,daga farkon rikicin Siriya zuwa ƙarshen watan Desemba an haƙiƙance mutuwar mutane 5.400, sannan fiye da dubu 10 suka ji raunuka,kuma a yanzu haka, gwamnati na tsare da mutune dubu 18 a cikin gidajen kurkuku.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita Saleh Umar Saleh