1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

August 13, 2011

Har yanzu dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da ɗaukar matakan ba sani ba sabo akan masu boren ƙyamar gwamnati, duk kuwa da matsin lamba da ƙasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/12GAO
'Yan boren nuna adawa da gwamnatin SiriyaHoto: dapd

A matsayin matakin baya-bayan nan na ci gaba da ɗaukar matakan murƙuhe masu boren nuna adawa da gwamnati, dakarun Siriya sun auka wa birnin Latakiya da ke gaɓar tekun ƙasar. Hakan ta faru ne bayan da komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ba da sanarwar gudanar da taro na musamman domin duba halin da al'umar Siriya ke tsintar kansu a ciki, a ranar alhamis mai zuwa. Faransa da sauran ƙasashen Tarayyar Turai da ke da kujera a komitin suna ƙara saƙkaimi domin ganin gamayyar ƙasa da ƙasa ta ɗauki matakan ladabtar da shugaba Bashar Al-Assad.

A matsyin matakin ci gaba da yi wa Assad matsin lama, sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton a karon farko ta yi kira da a ƙaurace wa sayen hajojin ƙasar ta SIriya. Aƙalla 'yan zanga-zanga 20 suka mutu a hannun dakarun Siriya a ranar 13 ga watan Agust. To sai ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar duk kuwa da matakan da sojoji ke ɗauka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal