1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Niger Delta a Nigeria

Zainab A MohammadMarch 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7b

Kungiyar yan ta kifen yankin Niger Delta dake kudancin Nigeria,sunyi alkawrin sake yin sanadiyyar dakatar da fitar da danyan mai na kimanin miliyan a kowane yini,cikin wannan wata,acigaba da neman hakkinsu na albarkatun man da ake haka a yankin.

Tsagerun,wadanda ke kiran kansu masu neman yancin kai ,a yanzu haka dai suna cigaba dayin garkuwa da maaiklatan kamfanin man Shell Amurkawa biyu da dan Birtania guda.Tuni dai hare haren da suke kaiwa cibiyoyin hakar danyan man ya gurgunta adadin man da ake fitarwa daga Nigerian,dake kasancewa kasa ta 8 a jerin masu arzikin man petur a duniya.Kana a yau suka fitar da sanarwar sake durkusar da harkokin hakan man ,matukar baa biya musu bukatunsu ba.

Kamfanin mai na Shell dai ya rufe cibiyoyin gudanarwansa dake yammacin yankin Niger delta,wanda ya jagoranci rage yawan gangan mai dubu 455 dake fita daga yankin a kowace rana.A watan febrairun daya gabata nedai yan yankin Niger Delta suka sanar da dakile kashi 30 daga cikin 100 na yawan danyan man dake fita daga yankin.