1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Matasa masu aikin hakar zinari

July 6, 2021

Dubban matasan Jamhuriyar Nijar ne ke aikin hakar zinari a Tchibarakaten, yankin da gwamnatin kasar ta bayar da izinin aiki a wurin tun a shekara 2015.

https://p.dw.com/p/3w7aF
Ghana - Goldabbau
A kasashen Afirka da dama, matasa na rungumar sana'ar hakar ma'adanin zinariHoto: Getty Images/AFP/C. Aldehuela

A baya-bayan nan dai an samu wani yamusti a babban wurin tonon zinarin na Tchibarakaten da ke karkashin ikon da'ira Iferouane, lamarin da ya kai har da mutuwa. Tuni dai hukumomin jihar Agadez suka dauki lamarin da muhimmanci domin tabbatar da zaman lafiya. Rahotanni sun nunar da cewa, matsalar ta samo asali ne yayin da ake son kwace wa wani matashi da 'yan uwansa da ke aiki a karkashinsa wurin aikinsu da suka shafe shekaru suna tonon zinari. A wani mataki na yayyafawa abin ruwan sanyi dai, tuni shugaban da'irar ta Iferouane Adam Efad da tawagar da ta mara masa baya, sun isa Tchibarakaten domin tataunawa da al'ummar yankin tare da daukar matakin kawo zaman lafiya.