1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Masar ya ɗauki hankalin duniya

February 5, 2011

Man'yan shugabannin duniya dake taro kan tsaro, sun maida hankali bisa yadda rikicin ƙasar Masar zai iya shafar duniya baki ɗaya

https://p.dw.com/p/10BRI
Frai ministan Birtaniya David Cameron ke tattaunawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, yau lokacin taro kan tsaro a duniyaHoto: dapd

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ƙira ga sauyin gwamnati a ƙasar Masar cikin zaman lafiya da kuma lumana. A lokacin da take yin jawabi ga taron tabbatar da tsaro a duniya dake gudana a birnin Munich na kasar Jamus, Merkel ta ce ƙungiyar Tarayyar Turai na son ƙulla ƙawancen da zai tallafawa duk wani canjin da za'a samu a ƙasar ta Masar. Akan hakane ta ce ta tattauna da sakatariyar kula da harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, domin yin aiki tare wajen neman masalaha ga batun sauyin gwamnatin. Ana jawabin Hillary Clinton cewa ta yi, amfani da damar da ta samu a wajen taron ne ya sa ta yin ƙira ga gudanar da zaɓe cikin adalci a ƙasar ta Masar, wanda ƙungiyoyin sa'ido akan zaɓuka a duniya za su yi na'am da shi. Hakanan a gefen taron tsaron na birnin Munich za'a gudanar da taron gungun ƙasashen da ke shiga tsakani a rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya, wanda ya ƙunshi ƙungiyar Tarayyar Turai, da Amirka da Rasha da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya. Kazalika a wajen taron ne sakatariyar harkokin wajen Amirkar za ta gana da takwaran aikin ta na Rasha Sergei Labrov, inda za su yi musayar takardun bayanan da suka shafi sabuwar yarjejeniyar da suka ƙulla, akan buƙatar rage yawan makaman nukiliyar ƙasashen biyu.

Mawallafi Saleh Umar Saleh

Edita: Usman Shehu Usman