1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Masar na ƙara yin muni

August 7, 2013

Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da ƙarfi wajen kawo ƙarshen zanga-zanga da zaman durshin da magoya bayan Mursi ke yi.

https://p.dw.com/p/19Lin
Hoto: Reuters

Fira ministan ƙasar Hazem Al-Beblawi ya sha alwashin kawar da 'yan ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi da ƙarfi daga zanga-zangar da suke gudanarwa kan nuna adawa da kifar da gwamnatin Mohamed Mursi da sojoji suka yi. Gwamnatin ƙasar da ke samun goyon bayan rundunar soja, ta ce, majalisar gudanarwa ta amince da daukan matakin na amfani da karfi.

Tun farko fadar shugaban ƙasar ta ce, hanyoyin diplomasiya na warware rikicin ƙasar sun ci tura, sannan ta yi gargaɗin cewar ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta hamɓararren Shugaba Mohamed Mursi ke da alhakin duk wani abin da zai biyo baya. A cikin wata sanarwa fadar Shugaba Adly Mansour ta ce, rashin samun nasarar warware rikicin ta hanyar diplomasiya, ka iya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasar, wanda zai iya shafan wasu ƙasashe musamman na Larabawa da Isra'ila. Ranar 3 ga watan jiya na Yuli sojoji suka kifar da gwamnatin ta Masar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane