1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya

March 15, 2011

Kasashe masu karfin tattalin arziki na G8 sun yi watsi da shirin daukar matakan soji a Libiya

https://p.dw.com/p/10ZcU
Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, da takwarar sa na Faransa Alain Juppe, A taron ministocin a birnin ParisHoto: dapd

Jamus da sauran kasashen dake kungiyar kasashe takwas masu karfin tattalin arziki sun yi watsi da shirin ɗaukar matakan soji akan Libya. A mai makon haka sun juya kan Majalisar Dinkin Duniya akan ta ƙara matsin lamba wa shugaba Muammar Gaddafi. Ministocin harkokin waje na kungiyar G8 sun gudanar da taro ne a binrin Paris, inda Faransa da Britaniya ke matsin lamban wajen ganin cewar MDD ta amince da sanya dokar haramta shawagin jirage ta sararin samaniyan Libya, domin kawo karshen hare haren da Dakarun Gaddafi ke kaiwa. Sai dai ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yana mai ra'ayin cewar ɗaukar matakin soji ba shine mafita ba, kuma Jamus bata muraɗin tsoma kanta cikin yakin yankin arewacin Afrika, kuma ya yi bayani kamar haka.

"A gani na wannan bai dace ba , domin ya kamata ayi tunani kafin daukar ko wane mataki. Haramta shawagin jirage ta sararin samaniya, na nufin ɗaukar matakan soji, kuma hakan ba shine abu daya dace wa saufuri ba".

A halin da ake ciki dai Dakarun Gaddafi na cigaba da luguden wuta a yankunan 'yan adawa guda biyu, a yaƙin yankin gabashin kasar daya doshi birnin Benghazi.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Usman Shehu Usman