1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU za ta yi taro kan tsaro

Abdul-raheem Hassan
February 9, 2020

Shugabannin kasashen Afirka za su tattauna a taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka karo na 33 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha kan samar da mafita a rikicin kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/3XTyJ
African Union summit
Hoto: Getty Images/I. Sanogo

Jigon taron na kwanaki biyu shi ne jaddada fatan kungiyar Tarayyar Afirka AU na kawar da yaduwar bindigogi da makamai a nahiyar Afirka nan da shekarar 2063, matakin da kungiyar ta dasa damba a 2013 da zimmar farfado da ingantaccen tsaro a kasashen Afirka.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai halarci taron don neman mafita kan rikicin Libiya. Ana kuma kyautata zaton taron zai karkare da cimma sauya shugabancin AU daga Masar zuwa Afirka ta Kudu.