1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Libiya na ɗaukar sabon salo

March 7, 2011

Ƙasashen Larabawa shidda da ke yankin gulf, sun yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ɗauki matakai wajen kare fararen hula daga tashe-tashen hankulan da ke afkuwa a ƙasar Libiya

https://p.dw.com/p/10Uve
Hoto: picture alliance/dpa

Minisatan harkokin wajen haɗaɗɗiyar daular larabawa Sheikh Abdullah bin Zayed al Nahayan ya yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniyar ne, a lokacin ƙaddamar da taron ministocin wajen ƙasashen, wanda aka fara yau a birnin Abu Dhabi.

A wannan Litinin dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a samar da dala milliyan 160 a matsayin taimakon jinƙai zuwa ga ƙasar ta Libiya, domin shawo kan mawuyacin halin da mafi yawancin yankunan ƙasar ke ciki inda kuma ta aika da tawagar da za ta yi nazari a kan halin da ƙasar ke ciki.

A yayin da ake fama da taɓarɓarewar tsaron da sojojin ke bayar wa a Libiyar, wanda kuma ke barazana ga rayukan al'ummar, ƙasashen ƙetare na bada shawarar tabbatar da cewa an haramta tashin jiragen yaƙi saboda a sami hanyar dakatar da jiragen yaƙin gaddafi.

Babban sakataren ƙungiyar ƙawance ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce babban ƙalubalen, shi ne a iya shawo kan hallakar da fareren hula ke yi a ƙasar. Kuma ya yi bayani kamar haka "idan har aka cigaba da kai irin wannan hare-haren a kan mutanen Libiyan, duk yadda aka yi, dole ne ya zamanto cewa an aikata laifukkan kisan ƙare dangi."

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal