1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kuɗin ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin Euro

August 11, 2011

Shugabannin Jamus da Faransa za su sake ganawa akan rikicin bashin dake addabar wasu ƙasashen Turai

https://p.dw.com/p/12FLS
Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa tare da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

Shugaba Nikolas Sarkozy na ƙasar Faransa ya buƙaci ganawa tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel domin tattauna matsalar bashin daya yiwa wasu ƙasashen Turai dake yin amfani da takardar kudin Euro katutu - a dai dai lokacin da kasuwannin hada-hadar kuɗaɗe na duniya ke fuskantar koma baya. Ofishin shugaba Sarkozy ya fitar da wata sanarwar dake cewar, a ranar Talatar dake tafe ne, Merkel za ta isa birnin Paris na ƙasar Faransa domin gudanar da taron, wanda ke da nufin samar da shawara ta bai-ɗaya game da hanyar tafiyar da mulki a ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗin Euro, gabannin ƙarshen lokacin bazara. Wannan sanarwar ta zo ne a dai dai lokacin da kasuwannin hada -hadar kuɗaɗe a ƙasashen duniya daban daban ke yin tangal-tangal bisa damuwar da suke nunawa game da cewar matsalar bashin daya kaiwa Amirka iya wuya ka iya jefa duniya cikin wata sabuwar mummunar matsalar tattalin arziƙi.

Fargabar da ake da ita na cewar ƙasashen Italiya da Spain ba za su iya biyan basussukan dake kansu cikin wa'adin da aka ajiye ba, ita ce ke ruruta rikicin kudin da Turai ke fama shi.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umar Aliyu