1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salon rikici kan kogin Nilu tsakanin Sudan da Masar.

Zainab Mohammed Abubakar AMA
June 23, 2020

Ethiopiya na son cike kogin Nilu duk da cewar ba ta cimma wata yarjejeniya da Sudan da Masar ba a yayinda cimma matsaya kan yawan ruwan da tashar samar da wutar lantar mafi karfi a Afirka ta ci tura.

https://p.dw.com/p/3e9TP
Äthiopien Addis Abeba | Diskussion Blue Nile & Renaissance-Damm | Flaggen
Tutar kasashen Ethiopiya da Sudan da Masar masu takon saka kan kogin NiluHoto: DW/G. Tedla

Masar na neman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya tsoma baki wajen warware matsalar kogin Nilu da aka jima ana kai ruwa rana a kanta. Masar na fargabar cewar shirin Ethiopiya na cike ma'ajiyar ruwan kogin na iya rage yawan ruwan da kogin zai samar.

Tun a shekara ta 2010 ne Ethiopiyar ta fara aikin ginin katafaren tashar samar da wutar lantarkin da zai lakume tsabar kudi dalar Amurka biliyan 4, kuma ake saran kammalawa a shekara ta 2022. Da farko dai an shirya cike dam din nan da watan Yuli, acewar mahukuntan na Addis Ababa.

Tsawon shekaru kenan aka gaza cimma warware matsalar Kogin na Nilu. Kuma tattaunawar baya bayannan ta kare baran-baran tsakanin kasashen Ethiopiya da Masar da Sudan. Wannan dai babbar matsala ce ga harkokin tsaro a yankin a cewar Dawid Wolde Giorgis na cibiyar nazarin lamuran tsaro da ke birnin Addis Ababa inda ya ce "Sabanin da muke gani tsakanin Ethiopia da Masar ba batu ne da ya dace a barwa kasashe biyu kadai ba, saboda zai shafi harkokin tsaro na yankunan da ma nahiyar Afirka gaba daya". Wannan takaddama da ma rashin gano bakin zaren warwareta, ya takawa Ethiopiyan birki a kokarinta na zama kasar data fi kowa fitar da kaya ketare, ita kuwa masar na ganin cewar, cike kogin da gaggawa na iya takaita yawan ruwan da zai samar.

Assuan-Staudamm in Ägypten
Wani bangare na kogin Nilu a MasarHoto: imago/Harald Lange

Masar za ta yi asarar kaso 22 na ruwan da take samarwa  Cike kogin na nufin Masar za ta yi asarar kaso 22 daga ruwan da take samarwa, kana akwai fargabar kaso 30 na filayen nomanta na iya rikidewa zuwa sahara. Masar da Ethiopian sun tsegunta yiwuwar daukar matakan soji domin kare muradun kowannensu, kuma kwararru na tsoron rushewar tattaunawar na iya jagorantar fadawa wannan rikici. Tuni dai Sudan da ke cikin wannan takaddama, ta sinci kanta cikin wadi na tsaka mai wuya.

A cewar William Davison na kungiyar sasansa rigingimu na kasa da kasa wajibi ne dukkan bangarorin biyu su koma teburin warware wannan matsalar yana cewa "Ko Ethiopiya ta fara cike kogin, babu tabbas game da hakan, saboda cikewar zai kasance ne a tsakiyar Juli, amma ko akasin hakan aka samu, yana da muhimmanci bangarorin su koma teburin tattanauwa domin magance matsalolin da ke kasa". Zuwan damuna a yanzu hakan ya kawo karin ruwa zuwa cikin bangaren kogin Nilu mai launin bula.Kuma Addis na ganin cewar tsakiyar wata mai kamawa ne zai zame lokaci mafi dacewa na fara cike ma'ajiyar ruwan kogin. A gina katafaren ma'ajiyar zai ruwan ne domin daukar akalla mita biliyan 74 na ruwa.