1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Siriya na ci gaba da awun gaba da rayuka

October 3, 2012

Ana ci gaba da gumurzu a birnin Aleppo na kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/16JMI
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service Forces loyal to Syria's President Bashar al-Assad patrol at Tal-al-Zrazir neighbourhood in Aleppo city September 29, 2012. REUTERS/George Ourfalian (SYRIA - Tags: CONFLICT MILITARY)
Aleppo GefechteHoto: Reuters

Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta ƙasar Siriya ta zargin sojan ƙasar da kaddamar da farmaƙi kan ynakin Qudsaya da ke yammacin Damascus babban birnin ƙasar.

Daraktan ƙungiyar ta kare haƙƙin bil Adama Rami Abdel Rahman, ya ce an kama mutane masu yawa yayin samamen.

Akwai rahotanni da ke cewa aƙalla mutane 31 sun hallaka sakamakon wasu fashe fashe cikin garin Aleppo birnin na biyu mafi girma. Dakarun gwamnatin ƙasar ta Siriya sun kwashe makonni su na ɗauki ba-daɗi da 'yan tawaye masu neman kwace iko da birnin na Aleppo.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal