1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Rikicin yankin Tigray na Habasha ya kazance

Abdullahi Tanko Bala SB
November 3, 2021

Yanayin da ake ciki Tigray na kasar Habasha ya yi muni matuka babu ruwan sha mai tsabta haka babu wutar lantarki sannan an toshe hanyar kai gudunmawar jinkai. Kasar dai na fuskantar annobar yunwa.

https://p.dw.com/p/42Wpv
Symbolbild Äthiopien Tigray-Krise | Ausnahmezustand
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

 

Wannan yanayi dai ya samo asali ne daga fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da mayakan aware na yankin Tigray da kuma luguden wuta ta sama da ake yi a Mekele babban birnin yankin Tigray. An kashe dubban jama'a fararen hula sannan ga fyade da kuma mutane da aka kame, masu rajin kare hakkin bil Adama sun yi kashedin cewa lamarin na zama tamkar yunkurin kakkabe wata kabila daga doron kasa.

Wani rahoton bincike na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar kan kan cin zarafin al'umma a yankin Tigray ya ce dukkan bangarorin sun aikata laifi, sojojin gwamnati da mayakan yankin Tigray.

Symbolbild Äthiopien Tigray-Krise | Ausnahmezustand
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Rikicin na kara fadada an ruwaito barkewar fada a wasu yankuna na kan iyaka fatan samun saukin lamarin na gushewa inda ake fargabar barkewar yakin basasa.

Farfesa Mulugeta Gebregziabher wani dan yankin Tigray dake Jami'ar Carolina a kasar Amirka ya kafa kungiyar agaji da ke taimakawa musamman a fannin lafiya a arewacin Habasha. Ya baiyana halin da ake ciki da cewa ya yi muni matuka. Yana mai cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza wajen magance lamarin.

Abin tambaya shi ne ta yaya aka yi wannan rikici ya faru a Habasha inda shugaban kasar  Abiy Ahmed ya sami lambar yabo ta zaman lafiya a 2019 bisa kokarinsa na sasanta kasar da makwabciyarta Eritrea? Wannan dai ba komai ba ne illa gwagwarmayar madafan iko tun bayan da Abiy wanda dan kabilar Oromo ne ya karbi mulki.

Äthiopien | Mekele | Verwundete äthiopische Gefangene im Mekele Rehabilitation Center
Hoto: AP Photo/picture alliance

A lokacin da ya karbi mulki a 2018 ya yi nasarar kakkabe 'yan kungiyar cigaban al'umar Tigray TPLF daga gwamnati ya kuma yi alkawari kawo gyara. Kasar Habasha wadda ke da yankunan kabilu har kimanin goma, an dade kusan shekaru 30 yan Tigra da kuma kungiyar TPLF suna jan ragamar shugabanci a siyasa da hukumomin soji ba kawai a arewacin Habasha ba har a fadin kasar baki daya, a saboda haka wasu ke ganin salon mulkinsa kamar na kama karya.

A daya bangaren Yonas Adaye daraktan cibiyar zaman lafiya da tsaro da ke Addis Ababa ya ce ya kamata kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta shiga cikin lamarin wajen samo mafita ga rikicin ba tare da katsalandan daga kasashen Yamma ba.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta kaddamar tawagar da za ta shiga tsakani karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. Sai dai kungiyar al'ummar Tigray sun fara fitar da tsammani a kan kasashen duniya na magance matsalar. Sai dai kamar yadda suka ce sun koma ga addu'a domin neman daukin mahalicci.