1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Cadi da Sudan

December 27, 2005

A yunkurinsa na shawo kan kungiyar tarayyar Afirka wajen yin Allah wadai da Sudan dangane da zargin da yake yi mata na shirin kai wa kasarsa farmaki, shugaba Idriss Deby na kasar Cadi, ya kai ziyara a Najeriya, inda ya gana da shugaba Obasanjo, a matsayinsa na jagoran kungiyar ta AU. A lokaci daya kuma, kungiyar AUn ta tura tawagarta zuwa manyan biranen kasashen biyu don ta gano wa idanunta yadda ababa ke wakana a kasa a can.

https://p.dw.com/p/Bu2z
Idriss Deby, shugaban kasar Cadi.
Idriss Deby, shugaban kasar Cadi.Hoto: AP

A yunkurin da yake yi na shawo kan Kungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, da ta yi Allah wadai da harin da yace Sudan na shirin kai wa kasarsa, shugaba Idriss Deby na kasar Cadi, ya gana da shugaba Francois Bozize na Jumhuriyar Afirka Ta Tsakiya jiya a birnin N’djamena, inda ya bayyana masa cewa, tun ran 18 ga wannan watan ne gwamnatin birnin Khartoum ta tallafa wa `yan tawayen Cadin da ke tsugune a Sudan din, kai wa kasarsa hare-hare guda biyu a garin Adre da ke kan iyakar kasashen biyu.

A yau ne kuma, shugaban na Cadi, ya kai ziyara a Najeriya, inda ya gana da shugaba Olusegun Obasanjo, wanda a halin yanzu shi ne kuma ke jagorancin kungiyar AU, don ya bayyana masa irin barazanar da yake ganin Sudan din na yi wa kasarsa. Da yake yi wa maneman labarai jawabi, bayan ganawarsa da shugaba Obasanjo a gonarsa ta Ota Farm a jihar Ogun, shugaba Deby ya ce: „na zo ne in daukaka kara gaban jagoran Kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu game da barazanar da Sudan ke yi wa Cadi.“ Ya kuma nanata adawar kasarsa, ga karbar bakwancin taron kolin kungiyar AUn, da Sudan za ta yi daga ran 23 zuwa 24 na watan Janairu mai zuwa. Da yake masa tambayoyin maneman labarai, Deby ya ce zai shawarci kungiyar da ta soke taron na birnin Khartoum, sa’annan kuma ta bar Obasanjo ya zarce da jagorancinta, maimakon ta mika wa shugaba Omar Hassan el-Bashir na Sudan ragamar jan akalar harkokinta bayan taron kolin. Bisa al’ada dai, bayan duk wani taron kolin Kungiyar ta AU, shugaban kasar da ta karbi bakwancin taron ne ke zamowa jagoranta, har zuwa lokacin gudanad da wani sabon taron kuma. Ta hakan ne dai, idan aka gudanad da taron a birnin Khartoum, kamar yadda aka shirya, shugaba al-Bashir zai zamo sabon jagoran kungiyar.

A halin yanzu dai, shugaba Obasanjo bai bayyana matsayin da ya dauka a kan wannan batun ba tukuna. Amma masharhanta na ganin cewa, hauhawar tsamari tsakanin Cadin da Sudan, zai kasance wani sabon kalubale ne ga kungiyar ta AU, wadda tuni take ta fama da sasanta rikice-rikce a yankuna da dama na nahiyar, kamar a Côte d’Ivoire, ko kuma tsakanin Habasha da Eritrea.

Tuni dai Kungiyar ta AU, ta tura wata tawaga daga kwamitinta na zaman lafiya da tsaro zuwa manyan biranen kasashen biyu, wato N’djamena da Khartoum, a wani yunkuri na kwantad da kurar rikicin, kafin al’amura su tabarbare.

A cikin wata fira da ya yi da sashen faransanci na nan gidan rediyon Deutsche Welle, kakakin tawagar, Malam Hassan Bâ na kasar Senegal, ya bayyana makasudin ziyarar ne da cewa:-

„Wajibi ne ga Kungiyar AUn da ta ga cewa an samad da zaman lafiya tsakanin kasashe mambobinta. Saboda ba za a iya tinkarar sake gina nahiyar da inganta halin rayuwar al’ummomminta, ba tare da tabbatad da zaman lafiya cikin lumana tsakaninsu ba. Abin da ya sa kuwa ke nan, wannan hauhawar tsamari da aka samu tsakanin kasashen biyu mambobin kungiyar, ta zamo abin damuwa, har ya kai ga tura wannan tawagar, don ta yi kokarin kwantad da kurar rikicin.

Q: To ko yaya tattaunawar da tawagar ta yi da mahukuntan kasashen biyu ta kasance?

Malam Hassan Bâ, ya bayyana cewa:-

Tawagar dai ta sadu da jami’an kasashen biyu ne don ta ji kararrakinsu tukuna. Ta hakan ne za a san abin da ke wakana takamaimai a kasa. To, daga bisani ne kuma, tawagar z ata mika rahoto kan ganowar da ta yi ga Hukumar kungiyar AUn.

Q: To ko wannan rikicin ba zai iya janyo cikas ga taron kolin kungiyar AUn da aka shirya yi a birnin Khartoum ba?

„Kawo yanzu dai, kome na tsaye ne kamar yadda aka tsara, wato za a gudanad da taron ne abirnin Khartoum. A nawa ganin dai, tun da an riga an yarje kan hakan, babu abin da zai kuma janyo wani cikas ga shirin.“

Q: Har ila yau dai, wannan rikicin zai kasance cikin muhimman ababan da ajandar taron za ta kunsa ne, wadanda za a tattauna a kansu ?

„Babu shakka, a ko wane taron koli na Kungiyar AU, ana tattauna matsalolin da ke kunno kai ne a wannan lokacin. Idan matsalar ta ki ci ta ki cinyewa har zuwa lokacin taron, to lalle ne za a yi shawarwari a kanta. Idan kuma kafin lokacin an shawo kanta, to sai a mai da hankali ke nan kan wasu matsalolin masu tsamari.“