1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Burundi da samar da hasken wutar lantarki a Kenya

Mohammad Nasiru AwalAugust 7, 2015

Halin zaman dar-dar a Burundi da sabuwar dokar kare muhalli a Kenya sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/1GBly
Beerdigung von Oppositionsmitglied Emmanuel Ndayishimiye in Burundi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Hari a kan sanannen mai kare hakin dan Adam a Burundi inji jaridar Die Tagsezeitung a labarin da ta buga game da halin rashin sanin tabbas da ake ciki a kasar ta Burundi.

Ta ce an yi wa daya daga fitattun masu fafatukar kare hakin dan Adam a Burundi, Pierre-Claver Mbonimpa mummunan rauni a wani hari da aka kai masa da nufin halaka shi. Shi dai Nbonimpa ya kwashe shekaru da yawa yana fafatukar kare hakokin wadanda ake fatattarsu a fagen siyasa da kuma wadanda 'yan sanda ke cin zarafinsu. Tun a shekarar 2001 ya kafa kuma yake jagorantar wata kungiyar kare hakin dan Adam da firsinoni. A wata hira da wannan jarida ta Die Tageszeitung ta yi da shi gabanin zaben shugaban kasar da aka yi ta kai ruwa rana kai, mai fafatukar kare hakin dan Adam din ya zargi 'yan bangar jam'iyyar da ke jan ragamar mulki da aikata ta'asa a kan 'yan kasar sannan ya yi nuni da yiwuwar barkewar wani yakin basasa a kasar. Ana zargin cewa an kai masa harin ne don daukar fansar kisan da aka yi wa tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar ta Burundi Adolphe Nshimi-rimana a ranar Lahadi da ta gabata.

Yiwuwar barkewar yakin basasa

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta labarto 'yan adawar kasar ta Burundi na nuna bukatar raba madafun iko ko kuma su dauki makami, abin da ka iya jefa kasar cikin wani yakin basasa inji jaridar.

Burundi Pierre-Claver Mbonimpa Menschenrechtsaktivist
Pierre-Claver Mbonimpa mai fafatukar kare hakin dan Adam a BurundiHoto: Getty Images/AFP/A. Vinceno

Ta ce ko bayan zaben da aka gudanar har yanzu Burundi na fuskantar matsaloli masu yawa. Ko da yake a hukumance shugaba Pierre Nkurunziza ya lashe zabe da kimanin kashi 69 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, amma kasar da ke yankin gabashin Afirka tana nesa da samun kwanciyar hankali a siyasance. Saboda haka a cewar jaridar wannan wa'adin mulki na uku mai cike da rudani ga shugaban mai shekaru 51, ka iya haddasa tashe-tashen hankula.

Hasken wutar lantarki ga kauyuka

Sabuwar dokar kare muhalli za ta rage fid da gurbatacciyar iska kana za ta sabunta hanyoyin samar da makamashi a kasar Kenya, inji jaridar Neues Deutschland.

Bildergalerie Solarenergie - Mali
Haskaka kauye da na'urar solarHoto: AFP/Getty Images/H. Kouyate

Ta ce kananan nau'rorin samar da hasken wutar lantarki ta amfani da zafin rana na samun karbuwa tsakanin mazauna yankunan karkara na kasar Kenya. To sai dai da yawa daga cikin al'ummomin karkarar da ke fama da karancin kudin shiga, ba sa iya saya saboda tsadarsu. A saboda haka majalisar dokokin Kenya ta amince da wata doka da za ta kawo saukin samun wadannan na'urorin masu amfani da zafin rana don samun hasken wutar lantarki. Jaridar ta ce da zarar shugaban kasa Uhuru Kenyatta ya sanya hannu kan dokar kare muhallin da ke zama wani bangare na aiyukan raya kasa, zan a samu ingantuwar hanyoyin samun hasken wutar lantarki a kasar ta Kenya da ke gabashin nahiyar Afirka.