1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin bayan zaɓe a Mexico

July 8, 2012

Enrique Pena Nieto, ɗan takarar shugaban ƙasar da hukumar zaɓen ƙasar ta tabbatar ya lashe zaɓen na fuskantar adawa daga al'umma, waɗanda ke zargin jamiyyarsa da tabka maguɗi

https://p.dw.com/p/15Tcv
Demonstrators shout slogans as they gather at the Zocalo Plaza in Mexico City, Saturday, July 7, 2012. Tens of thousands marched in rejection of the final count in the presidential election showing former ruling party candidate Enrique Pena Nieto as the victor. They believe the PRI engaged in vote-buying that illegally tilted millions of votes. PRI officials deny the charge. (AP Photo/Marco Ugarte)
Masu zanga-zangaHoto: AP

Dubun dubatan masu zanga-zanga suka fantsama kan titunan babban birnin Mexico ranar asabar domin nuna adawa da nasarar an takarar shugaban ƙasar Enrique Pena Nieto. Masu zanga-zangar na zargin cewa jamiyyar Pena Nieto ta Institutional Revolutionary Party wato PRI ta bayar da abinci kyauta, da katunan sayayya a manyan shaguna, da ma wasu mahimman kyautai masu ƙayatarwa ga jama'a, kafin zaɓen da aka gudanar ranar ɗaya ga watan Yuli.

Hukumar zaɓen Mexico to riga ta tabbatar da nasarar Peno Nieto tun ranar juma'ar da ta gabata, inda ta bayyana cewa ratar kashi bakwai cikin 100 ne ke tsakaninsa da abokin hammayarsa Andres Manuel Lopez Obrador. Wannan nasara ta Nieto ya maido mulki ga jamiyyar ta PRI wacce ta yi mulki a ƙasar na tsawon shekaru 70 kafin ta sha kaye a shekarar 2000 bayan da aka yi ta zarginta da murɗiyyar zaɓe da mulkin danniya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba

Edita:            Mohammad Nasiru Awal