Rikicin Amirka da Rasha kan Siriya na zafafa
April 11, 2018Talla
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi watsi da bukatar da Rasha ta bijiro da ita kan masu bincike daga kungiyar da ke fafutikar haramci da amfani da makami mai guba dangane da zurfafa bincike kan wanda ke da hannu a amfani da makamin mai guba a Douma da ke wajen babban birnin Siriya a karshen mako. Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya ya ce gwamnatin Shugaba Trump ce ke son kafar ungulu ga shirin bincike ta yadda za ta yi gaban kanta ta ce ga wanda ke da hannu wajen kai harin me guba a Siriya.
Amirka da Birtaniya da Faransa dai sun ki goyon bayan matakin na Rasha da suka ce matakin bai cika sharuda ba na sabbin hanyoyi da a ke bi wajen binciken amfani da makamai masu guba. Shugaba Trump dai ya ce za su kai wa 'yan ta'adda hari a Siriya.