1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Afghanistan na daukar sabon salo

Mouhamadou Awal Balarabe
August 3, 2021

Rundunar sojin Afghanistan ta yi kira ga mazauna Lashkar Gah da su tattara nasu ya nasu su fice daga garin, bayan mummunan fada da ya kaure da 'yan Taliban wanda ya salwantar da rayukan fararen hula 40.

https://p.dw.com/p/3yTsB
Afghanistan | Kämpfe zwischen Armee und Taliban
Hoto: Sanaullah Seiam/XinHua/dpa/picture alliance

Cikin wani sakon da ya nemi kafafen labarai su watsa cikin gaggawa, hafsan soji mafi girman mukami a kudancin Afghanistan Janar Sami Sadat, ya ce za su fuskanci 'yan Taliban domin su fatattake su ta ko halin kaka daga yankin. Saboda hake ya nemi mazauna Lashkar Gah da su kaurace wa matsugunansu.

Dama dai Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya bayyana damuwa a shafinsa na Twitter dangane da halin da fararen hular garin ke ciki, yana mai kira da a gaggauta kawo karshen fada a cikin birane. Sai dai kakakin ma'aikatar tsaron Afganistan, Fawad Aman, ya ce jiragen yakin Amirka sun kai hare-hare a Lashkar Gah, ba tare da sojojin Amurka a Afghanistan sun yi tsokaci a kai ba.

Tun dai bayan da Amirka ta bayyana aniyar kakkabe hannayenta daga harkar tsaro a kasar Afghanistan, 'yan Taliban da ke da tsattsauran ra'ayin addini ke mamaye garuruwa da dama na kasar.