1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Christen in Angst

September 26, 2012

Mu'amala tsakanin Kirista da musulmi a Masar na fuskantar koma baya.

https://p.dw.com/p/16FKC
Pastor Boulos Shehata zieht am Donnerstag (06.01.2011) bei einem Gottesdienst koptischer Christen zum Weihnachtsfest in Düsseldorf in die Kirche ein. Rechts im Bild der Vorsitzende des Rates Evangelischen Kirche in Deutschland (EKD), Nikolaus Schneider. Nach einem Anschlag auf eine koptische Gemeinde in Ägypten in der Silvesternacht findet der Gottesdienst unter Polizeischutz statt. Foto: Henning Kaiser dpa/lnw +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Cuɗayya tsakanin mabiya addinai daban-daban a Masar ta shiga wani yanayi na rashin tabbas da zargin juna,tun bayan da shugaban Mohammed Mursi ya hau karagar mulkin ƙasar.

Tun zamanin mulkin shugaba Hosni Mubarak an sha fuskantar saɓani da tashe-tashen hankula, tsakanin musulmi masu rinjaye a Masar, da kuma kirista mabiya ɗarikar Koptkik.Bayan da shugaba Muhamad Mursi ya yi nasara zama shugaban ƙasa kirista a Masar sun bayyana damuwa kasancewar sa jigo a ƙungiyar 'yan uwa musulmi mai tsautsauran ra'ayin kishin addinin Islama.Wata unguwa mai suna Imbaba dake birnin Alƙahira na daga yankunan da saɓani ya fi ƙamari tsakanin mabiya addinan biyu.A shekara da gabata,saidai musulmi a yayin zanga-zanga su ka ƙona wata coci dake cikin wannan unguwa.Hany Adli, kirista ne ɗan ɗarikar Koptik, ya bayana halin zullumin da suke rayuwa a unguwar Imbaba:

"Wannan unguwa mattatara ce ta masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama.Da dama daga cikinsu matasa marasa aikin yi wanda ba su yi wani dogon karatu ba.Wasu daga cikinsu nan suka girma wasu kuma da wayensu su ka zo.Suna koyan darrusa a nan.Suna taimakawa juna ta fannoni da dama.

1.Marymorkos Kirche in Schobra, Kairo..JPG Copyright Recht von Nelly Izzat DW(arabisch) Korrespondentin in Kairo. Schlagworte: Schobra, Kairo, Muslime, Kopten, Ägypten, Zusammenleben. Aufnahmedatum: Januar,2010, Schobra, Kairo
Hoto: DW

Idan mutum na fama da talauci ba shi da ko sisi,ba shi da cewa, doli ya bi ra'ayin wanda ke taimaka masa ko da kuwa tsatsauran ra'ayi ne, domin kuruciya ba ta tashi ɗanta yayi rarrafe."

A cewar Hany Adli rikicin addini da ƙasar Masar ke fama da shi ya samu asuli daga talaucin da ya mamaye ƙasar, domin kashi 40 cikin ɗari na al'umarta na raye cikin ƙazamin rashi.A ɗaya wajen, ya baiyana damuwa game da wa'azin nuna ƙyama ga addinin Kirista da wasu maluman ƙasar ke yi wanda kuma ke maida hannun agogo baya a yunƙurin cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin al'umar ƙasa:

"Haƙiƙa wannan abu ya na shiga rayuwata, to amma ƙaƙa na iya.Idan kawai sun yi sala ne su tafi babu damuwa domin kowa na da 'yancin yin addininsa, to amma matsala itace maimakon faɗakar da musulmin game da dokokin addinin Islama, sai malami yayi sa'o'i biyu cur, ya na wa'azin zage-zagen addinin kirista."

Ma'amala tsakanin mabiya addinin Kitrista da na Musulunci a Masar, ta ƙara taɓarɓarewa tun bayan Videon nan na tozarta addinin Islama da wani bayahude ya shirya a ƙasar Amurika,inji Mina Maha shima mazaunin aunguwar Imbaba dake birnin Alƙahira:

"Mabiya ɗarikar Koptik,tamkar ba su ci kasuwa ba ne runfa ke fada masu.Wasu matasa musulmi suna zargin cewar wani ɗan ɗarikar koptik ne ya sarrafa wannan video, saboda haka,a wani abu mai kama da kunburi ga doki sakiya ga raƙumi,suke huce haushi a gare mu."

Die Muslimbrüder oder Muslimbruderschaft (arabisch ‏الإخوان المسلمون‎ al-ichwān al-muslimūn) ist eine der einflussreichsten islamisch-fundamentalistischen Bewegungen im Nahen Osten. Sie wurde 1928 von Hasan al-Banna in Ägypten gegründet.

Cemma dai lokacin zaɓen shugaban ƙasa, mabiya addinin Kirista ba su zabi Mohamad Mursi ba,domin tunanin makomarsu idan ƙungiyar 'yan uwa musulmi ta hau karagar mulkin Masar.

To saidai shugaban ƙasar yayi alƙawarin kiyaye haƙƙoƙin dukan al'umar ƙasa ba tare da la'akari da addini ko wane ɓangaranci ba.

Kiristocin sun ce su na jira su gani a ƙas.

Mawallafa:Sailer Mathias/ Yahouza Sadisou Madobi
Edita: Umaru Aliyu