1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙasar Sudan

May 28, 2011

Tawagar jami'an gwamnatin kudancin Sudan ta fara tattaunawa da takwararta ta yankin Arewaci

https://p.dw.com/p/11Pse
Salva Kiir Shugaban yankin Kudancin SudanHoto: AP

Wata tawaga ta jami'an gwamnatin Kudancin Sudan ta isa birnin Khartum inda za ta tattauna da gwamnatin arewacin kasar dangane da saɓanin da ya biyo bayan mamaye yankin Abyei da sashen na arewacin ya yi yau mako guda kenan. Tawagar wacce ke ƙarkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar za ta gana da mataimakin shugaban ƙasar Sudan Ali Osman Taha.

Wannan ziyara ta bazata ta zo ne a daidai lokacin da ake fara tattaunawar sulhu a Adis Ababa kan yankin na Abyei mai arzikin man fetur da ɓangarorin biyu ke jayyaya akansa tsakanin Shugaba Omar Hassane El Beshir da jam'iyar National Congres Party ta shugaban ƙasar na yankin kudanci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.
Edita : Abdullahi Tanko Bala